Tare Da AMINA YUSUF ALI
Muna tafe da bayani a kan yadda mace ita ma za ta samar wa kanta girma da ƙima a wajen mijinta. Domin a baya mun yi magana aka girmama miji. To kada mu ɗauka namiji ne kaɗai yake buƙatar ƙimantawa da darajtawa a gidan aure. Ita ma mace tana buƙatar a ƙimanta ta. Da wannan nake cewa, a sha karatu lafiya.
Kamar yadda muka yi matashiya, ita girmama juna a gidan aure tana da matuƙar muhimmanci. Mace da namiji kowa na buƙatar girmamawa daga ɗanuwansa. Kuma girmama juna tsakanin ma’aurata yana sa zaman auren ya yi daɗi kuma ya zama mai ɗorewa.
Allah ya halicci mace da daraja da ƙima tun fil azal. Kuma ta cancanci mijinta da sauran mutane su girmama ta. Sai dai wani gudu ba hanzari ba. Shin ke kina girmama mijin naki yadda kike son ya girmama ki? Shin ke kanki kin cancanci wannan girman da kike so ki samu daga wajensa? Masu iya magana fa sun ce, sai ka bi fa, ake bin ka. Don haka idan kina so mijinki ya ƙimanta ki, to ki ninka biyayya da da’a, da girmamawa a gare shi.
Hanyoyin da za ki samar wa kanki ƙima a gurin mijinki:
Na farkon fari shi ne, idan har kika sayi rariya, to kin san za ta zubar miki da ruwa. Kuma da me kama ake ƙota. Wato idan kina son a girmama ki a zaman aure, to sai ki auri wanda kika san yana sonki, kina son sa. Kuma mutumin kirki da kika san ya san mutunci ba zai wulaƙanta ki ba. Soyayya tana taka muhimmiyar rawa a cikin kowacce mu’amala. Musamman ma ta auratayya. Sai yana son ki sannan zai dinga kallonki a matsayin abu mai daraja da zai mutunta.
Hakazalika, a yayin da yake zuwa gurinki zance kafin ki yi aure, za ki duba wanda yake girmama ki da iyayenki tun kafin ku shiga daga ciki. Amma wanda yake daka miki tsawa da zaginki, da yi miki ƙarfa-ƙarfa tun kuna waje, ba fa mijin aure ba ne. Don mutumin da kike gidanku bai girmama ki ba, ba yadda za a yi ya girmama ki yayin da kike ƙarƙashin inuwarsa da alfarmarsa. Yana ciyar da ke, da shayar da ke da sauran abubuwa. Sai a sake tunani.
Abu na biyu, kamar yadda na yi bayani a matashiya, sai fa kin girmama mijinki sannan zai girmama ki. Ki girmama shi wannan dokar Allah kika bi. Sannan kuma sanadiyyar haka shi ma zai ga naki girman. Sannan ki girmama duk wani abu nasa tun daga iyaye da dangi da duk ma dokokinsa har ma wasu harkoki da suka shafe shi. Ko baƙi ya ce zai yi ki zama mai girmama shi. Ko lokacin aiki da na hutunsa, da na cin abincinsa da sauransu, ki kiyaye.
Na uku, ki rage roqo da ba ni, ba ni. Yana rage ƙimarki ko ba a wajen miji ba, ko a wajen saurayi ne, da sauran mutane.
Na huɗu, Ki zama mai neman na kanta. Hakan zai sa ki rage dogaro da shi da roƙonsa yadda za ki ƙara ƙima a idonsa. Ke ma kina da harkokinki. Kina da biki, da sauran abubuwa. Tilasta masa ya yi abubuwa yana sa ya ji kin ishe shii. Kuma ya dinga kallon ki a mara daraja. Sannan kuma idan da halinki dinga taimakawa a gida. Hakan ma yana ƙara miki daraja.
Na biyar, kada ki dinga katse shi idan yana magana. Wannan alamar raini ne. Idan namiji yana magana ki dinga katse shi. Hakan na iya harzuƙa shi idan mai zuciya kurkusa ne. Shi ma ya yava miki maganar da ta fito daga bakinsa. Kamar dai yadda ke ma ba za ki ji daɗi ba idan ana katse ki idan kina magana. Musamman idan kina ganin mutumin yana ƙasa da ke ne.
Ki ba shi dukkan hankalinki a lokacin da kuke tattaunawa. Kada ki dinga danne-dannen waya ko wasu abubuwan a lokacin da mijinki yake buƙatar hankalinki. Idan so samu ne ma, har talabijin ki kashe ki saurare shi. Hakan zai sa shi ma ya dinga daraja buƙatunki kamar yadda kike daraja nasa.
Yi masa uzuri. Mijinki shi ma biladama ne da yake buƙatar uzuri da yafiya a lokacin da ya yi wani kuskure. Tayar masa da hankali da rashin karɓar uzurinsa yana sa shi ya ji ƙimarki ta ragu a idonsa. Yayin da ya yi wani abu da ya bata ranki, gara ma kinyi masa magana a cikin lumana yadda zai fahimta. Kin ga riba biyu, kin ƙara ƙima, kuma kun samu fahimtar juna.
Ki koya wa yaranki su yi masa biyayya. Yana da kyau ki koya wa yaranki biyayya ga mahaifinsu. hakan zai sa da ke da su ku zama ababaen alfaharinsa. Ko kuna da yawa wajen mijinku, za ki yi zarra a zuciyarsa idan kin ɗora yaranki a kan su san daraja da ƙimar mijin naku. Haka kuma da ma a tsarin tarbiyya, ya kamata ki koya musu yadda za su girmama na gaba da su.
Kada ki dinga kwatanta shi da sauran maza. Musamman ma waɗanda suka fi shi arziki ko kyau ko wani abu. Tare da hangen mazajen ‘yanuwanki da abubuwan da suke musu. Hakan yana rage miki ƙima a wajensa. Haka kuma zai ƙullace ki, ya ji haushinki.
Ki dinga ɓoye aibinsa a wajen sauran mutane. Kada ki zama mai fallasar da sirrin gidan aurenki a titi. Duk lokacin da zancen ya dawo kunnensa, ƙimarki da darajarki za su ragu a idonsa. Haka idan yabonsa kike yi, zancen ya dawo kunnensa zai ji daɗi kuma darajarki ta ƙaru a idonsa.
Kada ki kunyata shi, musamman a cikin mutane. Ki tuna ke ma fa ba za ki so a yi miki hakan ba. Ki dinga yi masa magana da daɗaɗan lafuzza.
Kada ki zama mai yawan ƙorafi. Mutane suna cewa, wai da ma mace an san ta da ƙorafi. Amma kuma ai ba kowacce mace ba ce mai ƙorafin. Ki yi ƙoƙarin fitar da kanki daga rukunin waɗancan mata masu yawan ƙorafi, in dai kina buƙatar girmamawa a wajen mijinki.
Kar ki yarda ki dinga takalarsa da faɗa a gaban yaranku. Hakan ma wata hanya ce ta rage miki ƙima a wajensa.
Ki dinga yaba wa ƙoƙarinsa tare da koxa shi. Ki dinga nuna masa shi ne tauraron da fi kowanne namiji a Duniya. Hakan zai ƙara miki ƙima a idanunsa.
Ki zama mai kula sosai da abubuwansa. Kada ki bari yara ko wasu su vatar ko lalata ko karya masa kayansa. Ko abu ya siyo don amfanin gida, kada ki lalata ko ɓarnatar da shi.
Ki dinga ba shi sarari a cikin gidansa. Takura masa da nanuƙarsa koyaushe yana rage qimarki a idonsa. Shi ma kamar yadda kike buƙatar sarari da rashin takurawa ko hutu ko rashin hayaniya a wasu lokutan, yana buƙatar hakan. Nuna masa kin fahimci hakan zai sa ya ƙara amincewa da sakankancewa da ke. Kuma idan akwai yarda, girmamawa ke biyo baya.
Ki dinga ba shi wuƙa da nama na tafiyar da zamantakewarku. Ki dinga karɓar hukuncin da ya yanke hannu bi-biyu a matsayinsa na shugaban. gidan. Za ki yi hakan ne ba wai don ke xin maqasqanciya ba ce a gidan. Sai dai don bin umarnin Ubangiji (SWT) na biyayya ga miji.
Kada ki dinga yi masa tufka da warwara a cikin tarbiyyar ‘ya’yansa. Yaran nan ba naki ne ke kaɗai ba. Da ke da shi kuka taru, kuka samar da su. Amma duk da kusancin an san yara sun fi sabo da uwa, saboda sun fi samun lokaci mai tsaho tare da ita. Amma shi ma uban ki dinga ba shi dama a cikin rayuwar yaran. Kada ki nuna masa bai isa ba, musamman a gabansu. Hakan zai ƙara miki qima wajensa.
Kada ki bijire wa buƙatarsa idan ya nema. Sai dai idan kina da wani ƙwaƙƙwaran dalili na hanawa. Rashin saurarensa a shimfiɗa yana rage ƙimarki a idanunsa. Sannan kuma hakan sava wa Allah ne.
Ki zama mai tsafta da gyara da ƙawata kanki a kullum. Hakan zai sa ya ƙara ganin ƙimarki kuma sonki ya ƙaru a zuciyarsa. Duk da dai an san kina da hidindimu na yara da aiki ko karatu ko sana’a idan kina yi. Amma ki samu lokacin yin gyara saboda shi.
Girmama danginsa Kamar yadda na faɗa a baya, rashin girmama danginsa ko matansa ko ‘ya’yansa da ba ke kika haife su ba, yana zubar miki da qima a idanunsa. Abinda za ki duba fa su waɗannan mutanen fa wani ɓangare ne na mijinki da yake ji da su. Kin ga ko son su zai ƙara miki ƙima a idonsa.
Neman shawararsa kafin ki aiwatar da abu yana sa ya ji ya gamsu da biyayyarki gare shi. Domin hakan yana nuna irin girmamawarki a gare shi. Hakan yana ƙara miki ƙima a idanunsa, sosai. Musamman idan kina ɗaukar shawararsa ki yi amfani da ita.
Hakan zai masa daɗi sosai kuma ba zai taɓa fasa saurarenki duk lokacin da kika zo neman shawara. Kuma sannan zai dinga neman taki shawarar a cikin lamurransa shi ma.
Ki zama mai yawan addu’a a gare shi da sauran iyalanki.
To ‘yanuwa mata, da fatan za ku yi amfani da waɗannan shawarwari domin samun girmamawar mijinki. Kada ki dinga jin kanki kina ganin dole namiji sai ya girmama ki a matsayin mace. A’a gara ki bi waɗannan dabaru don cimma wannan. Haka darajta mijinki a matsayinki na mace ba faɗuwa ba ce. Hakan yana nuna irin qarfin soyayyarki ga mijinki da kuma irin biyayyarki ga mahaliccinki ne.
Domin shi ya ce a yi biyayyar aure. Kuma Allah zai taimake ki saboda haka. Haka a wajen mijinki wallahi kin fi ƙarfin wulaƙanci da raini. Allah ya datar da mu. Masu kira da shawara da tsokaci da fatan alkhairi, muna godiya. Mu hau a mako mai zuwa a shafinsu na zamantakewa a jaridarmu mai farin jini ta Manhaja Blueprint. Na gode.
08024859793