Idan malamai ba su faɗa wa shugabanni gaskiya a kan mumbari ba, a ina za su faɗa?

Manhaja logo

Daga SALISU ISMA’IL KABUGA

Ita gaskiya, gaskiya ce indai gaskiyar ce.

Yayin da aka tozarta gaskiya, ko kuma sai an zaɓi wanda za a gaya wa gaskiya. Ma’ana, sai masu rauni (Talakawa) za a gaya wa gaskiya, babu shakka an tozartar da gaskiya.

Mecece gaskiya kuma a ina za a faɗi gaskiya? 

A taƙaice gaskiya nasiha ce, wadda ake faɗa wa mutum/mutane cikin zance ko a wa’azance kamar yadda malamai suke yi idan za su warware zare da abawa a kan wani abu, yayin da suke kan munbarin khudba da ma a kowanne zarafi da suka samu na feɗe gaskiya.

Irin wannnan muhimmin aiki na faɗar gaskiya, ana iya yinsa a ko’ina matuƙar akwai zarafin yin hakan. Kuma gaskiya ta kowa ce. Ma’ana, ana iya gaya wa kowa gaskiya tunda dai kamar yadda na ce a taƙaice, gaskiya nasiha ce. Ana iya yi wa shugabanni/Masu mulki da  masu kuci da kuma Malam talaka.

Me ye aibu idan an faɗi gaskiya? 
Matuƙar gaskiya gaskiyar ce, babu wani aibu ga dukkannin ɓangarori biyu wato ga wanda ya faɗi gaskiya da kuma wanda aka faɗa wa gaskiyar. Amma kuma ita gaskiya ɗaci gare ta. Domin ina iya tunawa yadda a waƙe, Marigayi Sa’adu Zungur ke faɗi. Muddun mutum ko mai wa’azi a kan gaskiya yake magana, to kuwa komai faɗin gaskiyar ya jawo, ta biya. Cewar Sa’adu Zungur cikin waƙensa.

Yadda malamai a dukkannin sassa suka daɗa zage ɗamara wajen tunasar da Shugabanni halin da ƙasa ke ciki na rashin tsaro da ƙuncin rayuwa da ake ciki a yanzu, abin a yaba ne. Domin duk ɗan’Adam ƙasashe ne a kodayaushe yana buƙatar a tunasar da shi game da yin abinda ya kamata. Kuma ina kyautata wa malaman nan zaton cewa, suna yi ne domin neman gyara.

A ce a wayi gari ana yi wa malamai barazarar raba su da wurare ko mumbarorin wa’azinsu, domin kawai suna isar da nasiha ga shugabanni kai tsaye daga inda suke da ikon aikewa da sako/wa’azi. Yin hakan tamkar komawa zamanin jahiliyya ne.

Masu cewa, Malamai ba za su yi wa shugabanni nasiha ko jan hankalinsu a kan munbarin karatu/Khuɗba ba, To a ina kuke so su yi? Shin kuna zaton duk wanda nasiha ba ta yi masa daɗi daga munbari ba, ya za a yi ta yi masa daɗin ji idan ga ka, ga shi a fadarsa? 

Shin ko kuma kuna ganin cewa su wadanda ke kewaye da shugabanni, da kuma ‘yan sa kai, wato ‘yan jagaliyar dake kewaye da shugabannin za su bar Malami ya samu ganin shi (shugaban) cikin karamci? Domin ni dai a iya sani na a halin da ake ciki ganin shugabanni musamman na siyasa ba sauqi. Balle shi ba a irin wannan yanayi da ‘yan ba ni na iya ke kewaye da fadar masu mulki domin kwaɗayin wani abu.

Haka kuma, ina kuka kai tunanin da mafi yawan mutane suke yi cewa, akasarin waɗanda shugabanni ke rufe ƙofa da su, sun je karɓar nasu kason ne musamman idan aka ga malami ne ?

A tambayi duk wani shugaba cewa ya yake ji, idan aka ce gashi can malam wane a kan munbarin karatu/khuɗubarsa yana fahimtar da jama’a game da wani abin alkhairi da shugaban ya yi, ko kuma ma a ce ga shi can yana yi masa addu’a tare da ɗalibansa? 

Idan har yin hakan ba ƙetare haƙƙin iyakar malunta ba ne, To ta yaya yin wa’azi gare shi a kan ya gyara wani abu da yake damun Jama’a a kan mumbarin da a da aka yabe shi zai zama kuskure? Kuma idan har yabon da malamai ke yi wa shugabanni a kan mumbari yayin da suka yi abin yabo bai zama siyasa ba, ta yaya gaya musu cewa su gyara ya zama siyasa?

Dogaro da wannan nazari nake ganin, a ƙa’idance da ma kamata ya yi a ce malamai su dinga faɗin gaskiya kowacce iri ce yayin da suke kan mumbarin karatu/khuɗuba. Domin gaskiya ta kowacce, ala bashi idan hali ya ba su dama wataran sun rabauta da ganin shugaban da suka aikawa da saƙon a baya ta kan mumbari to sai ku ji tsoron Allah su ƙarasa aikinsu na faɗin gaskiya gaba da gaba kamar yadda ake yi wa ɗalibai.

A gaya wa duk wani shugaba dake ci ko ‘yan kanzaginsa, shin ba su san cewa su MALAMAI su ne magada Annabawa ba? Shin da ma akwai abinda addini bai yi magana a kansa ba? Ko kuma ya ware cewa ba za a yi magana a kansa ba?

Babban aikin Malamai shi ne shiryar da Al’umma wajen yin duk wani abu dai-dai (politics inclusive), yadda Allah ya ke so da kuma yadda rayuwar al’umma za ta inganta a duniya. Kuma idan aka ce al’umma ba ana nufin talaka ba kawai, har da shugabanni a kowanne mataki.

Idan har Malamai ba za su gaya wa Gwamnati da shugabanni inda suka gaza ba ko kuma abinda ya zama matsalar jama’a ba, to waye ya fi su wanda zai gayawa shugabannin indai har abinda ake tunasar da su gaskiya ne?

Mu yi hattara jama’a!

Ƙudurce jin haushin malamai a zuci kawai kan iya hana mutum cikawa da imani. Domin alamu ne na munafunci. Ballantana yunqurin hana malamai isar da saƙon gyarawa wanda aiki ne da Allah ya ɗora musu, saboda su ne masu shiryarwa, tun da dai a yanzu babu Annabawa.

Guje wa Malamai ko korar su daga Mumbarin wa’azantarwa ko shakka babu aikine irin na Ashararai, waɗanda suka sanya Duniya a gaba. Kuma irin waɗannan mutane da ‘yan kanzaginsu da a ce a lokacin Annabawa suka zo, wallahi irin su ne za ka ga suna fito-na-fito da Annabawan, ko ma su kore su daga gari.

Yana daga cikin alamun rashin rabo da taɓewa, ka ga mutum ya fito ƙarara yana faɗa da gaskiya, ko kuma yana kare ƙarya da kuma jin haushin duk abinda malamai ke faɗa na gaskiya.

Kowanne musulmi wakilin Allah ne a bayan ƙasa, kuma rayuwa ba ta wanzuwa sai kowannenmu ya amsa tare da isar da wakilcin dake kansa ta hanyar faɗin gaskiya da aiki da ita. Domin Allah ne da kansa ya umarci masu Imani da su kawar da mummunan abu da hannayensu, ko da bakunansu (wa’azi) ko kuma su ƙyamaci abin a zuciyoyinsu, wanda shi ne mafi raunin imani.

Babu shakka, halin da al’ummar Nijeria ke ciki a yanzu na ƙuncin rayuwa da rashin tsaro, wanda ya haifar mana da zullumi da firgici a birane da ƙauyuka, a yanzu ne ya kamata kowannenmu ya tashi wajen yin abinda zai iya. Ma’ana, shugabanni na yi, malamai na yi, talakawa ma na yi.

Haƙiƙa abin takaici ne matuƙa a ce a irin wannan lokaci da kusan kowanne ɗan Nijeriya, masu ƙarfi da raunana, waɗanda ke cikin rigar mulki da waɗanda ake shugabanta ke cikin rashin tabbaci saboda ba wanda ya tsira. Amma a ce wai a samu wasu daga cikin jama’a suna fushi da yadda malamai ke gaya wa gwamnati gaskiya a mumbarinsu har ma ta kai ga dakatar da wasu ko korar su, da sauya su da wanda zai yi akasin abinda wanda aka kora ya yi. Shin wai ma tsakanin fushin Allah da na shugaba, idan har ba a kan dai-dai yake ba, wanne ne abin tsoro? Kowanne Mai imani ya amsa wa kansa.

Wannan tana a matsayin irin gudummawar da zan iya bayarwa a matsayina na ɗan ƙasa da kundin mulkin Nijeriya ya sahalewa tofa albarkacin bakinsa. Kuma ban yi wannan rubutu da nufin musguna wa kowa da kowanne ɓangare ba, sai domin fatan ganin ƙasata (Nijeriya) ta samu zaman lafiya da bunƙasar arziki ga kowanne ɗan ƙasa. 

Allah ya fidda ƙasata daga halin da take ciki a yanzu na rashin tsaro da firgici a dukkanin garuruwan Arewacin Nijeriya, da ma sauran sassa na ƙasar nan da ma Duniya bakiɗaya. Barka da Azumi!
 
Kwamared Salisu Ismail Kabuga
Ɗan jarida daga Kano
[email protected]
08052529040

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *