Idin Ƙaramar Sallah: Dalilinmu na bijire wa Sarkin Musulmi, cewar Sheikh Lukwa

Daga BAKURA MOHAMMAD a Bauchi

Sheikh Musa Lukwa, Malamin addinin Musuluncin nan wanda ya jagoranci almajiran sa suka yi Sallar Eid-el fitr a ranar Lahadi maimakon Litinin kamar yadda Sarkin Musulmi ya umarta, ya yi kariya wa wannan manufa tasa.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, wanda shine jagoran ɗaukacin dukkan Musulmin ƙasar nan dai, ya ayyana ranar Litinin da ta gabata ta kasance ranar Eid-ul Fitr.

Sarkin Musulmi ya bayyana cewar, ba a bayar da labarin kamawar watan Shawwal, Shekaru 1443 Bayan Hijira ba a ranar Asabar, kuma bisa tabbacin za a tsinkayi watan a ranar Lahadi domin a ranar aukacin Musulman ƙasar nan za su cika yin azumi kwanaki talatin, ya ayyana cewar, ranar Litinin ta kasance ranar sallar Eid-ul Fitr, amma Sheikh Musa Lukwa ya ce matsayin na Sarkin Musulmi akan ranar Eid-ul fitr akwai savani a cikin sa.

“Wani Malami a Jami’ar Usman Ɗanfodiyo, Dokta Maigari shi ma ya tabbatar da ganin watan na Shawwal a ranar ta Asabar, kamar yadda al’ummomi daban-daban har guda goma a garin Jega ta jihar Kebbi suka tabbatar, kuma babban Limamin garin Jega, Malam Bashar ya tabbatar.
“Hakazalika Shehi Ɗahiru Bauchi ya gaskata da ganin sabon watan na Shawwal a ranar ta Asabar a wurare daban-daban masu yawa a cikin ƙasar nan.

“Saboda haka, muka gudanar da Sallar Eid-ul fitr domin koyi da umarnin Shugaban Halitta, Ma’aiki Sallallahu Alaihi-Wassallam na ɗaukar azumin watan sharu Ramadana idan an tsinkayi watan, kuma a ajiye azumi da zarar tsinkayar watan Shawwal.

Kuma ya zama wajibi mu yi wa shugabanni biyayya, musamman ma Mai Alfarma Sarkin Musulmi, domin yin hakan ya kasance tilas akan dukkan kowane Musulmi, amma da sharaɗin idan bai bijire wa umarnin Mahalicci Sarki Allah ba, da kuma Ma’aikin sa, Muhammad (SAW).

“Babu wata hujja da wani zai yi na’am da wata shawara ko umarni bisa dacewar kimiyya na masu ilimin taurari domin yin hakan ya sava wa addinin mu, kuma ko da Imamu Malik ya yi hani da yin hakan,” Shehi Lukwa ya shaida wa manema labarai.

Akan ko sun tuntuvi kwamiti da aka ɗorawa alhakin sanar da ganin wata, Shehi Lukwa ya bayyana cewar babu amfanin yin hakan, domin waɗancan mahukuntan sun rigaya sun yi hukuncin su.

Ya kuma yi waiwaye da cewar, makamantan waɗannan hujjoji sun gabata a can baya, amma kwamitin ya yi burus da su.

“A shekara ta 2011 makamancin wannan yanayi ya faru. An shaidar da ganin watan a wurare masu yawa, waɗanda a bisa ƙa’ida aka gabatar wa kwamiti, wacce da ta gabatar wa Mai Alfarma Sarkin Musulmi, ya yi wancakali da su. Dalili ma kenan da ya sanya shugaban kwamitin na wancan lokaci, Farfesa A.A Gwandu ya ajiye shugabancin kwamiti.

“Kuma akwai wani lokaci da aka tabbatar da ganin wata a yankin Mabera, kuma aka gabatar wa Dagacin Ƙauyen Mabera, wanda shi kuma ya gabatar wa Hakimin Gagi wanda ya yi ta kiran sakataren fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi ba tare da wani ba’asi ba.

“Hakimin sai ya rubuta wa Sarkin Musulmi, amma sai Sarkin ya mayar da martanin cewa, sabon watan zai kama ne kashegari ba wannan ranar ba. Ni kaina na ga martanin da Sarkin Musulmi ya rubuta. Ba za mu ji maganar wani wanda baya bin umarnin Mahalicci da Ma’aikin Sa (SAW) ba,” in ji Shehin.

Rahotanni sun yi nuni da cewar, wannan ba shine karo na farko da Lukwa ya bijire wa umarnin Sarkin Musulmi ba, ta hanyar yin jagorancin Sallar Eid-ul fitr.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *