Idon al’umma a kanku ya ke, ku riƙa adalci koyaushe – Shettima ga alƙalai

Daga BELLO A. BABAJI

Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya yi kira ga alƙalai da su ƙaurace wa ababen zargi tare da tabbatar da gaskiya da adalci a yayin ayyukansu, ranar Laraba.

Shettima ya bayyana haka ne a yayin lakcar buɗe zauren alƙalai na BoB a Abuja, inda ya ce al’umma na da maƙuran tunanin samun adalci daga gare su duk da cewa a wasu lokutan akan samu jinkirin yanke hukunci akan shari’o’i a sakamakon wasu uzururruka.

Ya ce, dokoki ababe ne da sai da su al’umma za ta zauna lafiya a yayin zamantakewa, don haka lallai sai an samu ingancin aiki a fannin shari’a.

Ya kuma ce, akwai buƙatar alƙalai su jajirce wajen tsaya wa adalci a kowane hali suka tsinci kawunansu, ta yadda al’umma za su amince da su wajen samun adalci a duk lokacin da suka gabatar da ƙara.

Shettima ya jaddada ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu na tabbatar da an samu fahimtar juna a tsakanin ɓangarorin gwamanti guda uku, wanda aciki akwai fannin Shari’a don ci-gaban demokraɗiyya da tafiyar da al’amuran ƙasa bisa tsari mai kyau.

Kazalika, ya taya su murna bisa ƙaddamar da rahoton Shari’a na BoB, wanda hakan ya nuna yadda su ke ƙoƙarin inganta harkar shari’a ta hanyar haɗa hannu a tsakanin su.