Idon Mikiya: Buhari ya tare wa Shugaban NIA faɗa da gidan rediyon Vision FM

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Gwamnatin Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ta dakatar da shirin ‘Idon Mikiya’, wanda wani shahararren shiri ne a gidan rediyon Vision FM da ke Abuja da wasu jihohin Arewa, saboda tattaunawa kan taƙaddamar tsawaita naɗin da aka yi wa Daraktan Hukumar Leken Asiri ta Ƙasa (NIA), Alhaji Rufa’i Abubakar, da kuma zargin rashin iya aikinsa, lamarin da wasu ke kallo a matsayin tare wa shugaban na NIA faɗa da gidan rediyon na Vision FM.

A cikin wata wasiƙa da ta aike wa Manajan Daraktan Gidan Rediyon Vision FM, wacce Blueprint Manhaja ta samu kwafi a ranar Laraba da ta gabata, Hukumar Kula da Kafafen Yaɗa Labarai ta Ƙasa (NBC) ta yi iƙirarin cewa, ta ƙaƙaba wa kafar yaɗa labaran takunkumi ne, saboda yaɗa labaran da ke cutar da tsaron Nijeriya a ɗaya daga cikin shirye-shiryenta mai suna ‘Idon Mikiya’, wanda aka gabatar ranar 5 ga Janairu, 2022.

Hukumar NBC ta yi nuni da cewa, gidan rediyon ya karya sashe na 39 (3) (b) na Kundin Tsarin Mulkin Ƙasar na 1999, wanda ya yi hani da tattaunawa kan al’amuran da suka shafi jami’an tsaro ko hukumomin tsaron gwamnati.

“Tattaunawar da ku ka yi kan batutuwa, ciki har da naɗe-naɗen da Hukumar Leƙen Asiri ta Ƙasa (NIA) ta yi, ya zama saɓa wa tanadin sashe na 39 (3) (b) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya na 1999, wanda ya sanya takunkumi kan al’amuran da suka shafi tsaron gwamnati da ayyukan hukumomin da doka ta kafa,” inji mai kula da harkokin yaɗa labarai na Nijeriya.

Sai hukumar ta ci tarar kafar yaɗa labaran zunzurutun kuɗi har Naira miliyan biyar tare da dakatar da shirin na Idon Mikiya tsawon watanni shida tun daga ranar 28 ga watan Janairun 2022.

Wasiƙar ta kuma yi iqirarin cewa, yaɗa irin wannan sirrin da sauran batutuwan da suka shafi hukumar tsaron ƙasa, wani abu ne da ke da alaƙa da tsaron ƙasa.

Sai dai kuma, wasu na hasashen cewa, wannan batu ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Buhari ke cigaba da ƙoƙarin daƙile kafafen yaɗa labarai na Nijeriya.

A watan Agusta na 2021, Babban Daraktan NBC, Malam Balarabe Ilelah, ya sha alwashin cewa, Gwamnatin Buhari za ta ci gaba da hukunta ’yan jarida da kafafen yaɗa labarai kan abin da suke yaɗawa. Ya yi gargaɗin cewa, za a hukunta duk wanda aka kama yana karya ƙa’idojin watsa shirye-shirye don bayyana kansu.

Idan za a iya tunawa, a watan Disambar da ya gabata, an ruwaito cewa, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙara wa’adin Rufa’i a matsayin shugaban NIA, duk da zanga-zangar cikin gida na nuna adawa da sake naɗa shi da aka samu.

Manyan jami’an NIA da masu sukar Gwamnatin Buhari sun soki naɗin Rufa’i a shekarar 2018 kum sun koka kan cancantarsa, kishin ƙasarsa da kuma dalilin da ya sa aka naɗa shi.

Daga cikin sukar naɗin Rufa’i aka yi shi ne, akwai yadda ya faɗi jarrabawar ƙarin girma da ya yi a matsayin darakta a lokuta daban-daban har sau uku kafin a yi masa ritayar dole.

Baya ga zargin Rufa’i na rashin cancantar zama babban jami’in hukumar ta NIA, wasu daraktoci a hukumar sun zargi Shugaba Buhari da ƙabilanci da ɓangaranci wajen sake naɗa shi. Tsawaita wa’adin na Rufa’i, wanda aka bayar a watan Nuwamba, ya fara aiki ne daga ranar 10 ga Junairu, 2022, bisa la’akari da ranar da aka fara naɗa shi shugaban NIA a shekarar 2018.