‘Idon Mikiya’: Matakin NBC ya fallasa take-taken gwamnati na neman daƙile ‘yancin faɗar albarkacin baki – CISLAC

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar nan mai fafutukar kare haƙƙin al’umma da aka fi sani da CISLAC a taƙaice, ta yi tir da matakin ƙaƙaba wa gidan rediyon Vision FM takunkumi da Gwamnatin Tarayya ta yi.

Gwamnatin Tarayya ta kafa wa tashar Vision takunkumi ne sakamakon tattaunawar da ta yi kan abin da ya shafi sake naɗa shugaban Hukumar Leƙen ta Ƙasa (NIN), Ahmed Rufai Abubakar a cikin wani shirinta mai taken ‘Idon Mikiya’.

Sai dai da alama wannan mataki da Shugaba Muhammadu Buhari ya ɗauka bai yi wa wasu jami’an tsaron hukumar da masu ruwa da tsaki da daɗi ba.

Wasu daga cikin jami’an NIA, sun bayyana a cikin wata wasiƙa da suka rubuta a can baya cewa Abubakar ya bar aiki a 2012, shekaru shida kafin naɗa shi a matsayin Darak-Janar na NIN.

Wasiƙar ta nuna cewa, “An yi masa murabus na dole bayan da ya faɗi jarabawar neman ƙarin girma har sau uku a jere, daga matsayin Mataimakin Darakta zuwa Darakta.

“Naɗin da aka yi masa ya haifar da mu’amala mara armashi a tsakanin babban daraktan da ƙananan daraktoci.”

NBC ta dakatar da shirin Idon Mikiya ne na tsawon wata shida daga ranar 28 na Janairun da ya gabata, tare da danƙara wa tashar tarar Naira miliyan biyar.

Cikin sanarwar da Daraktan CISLAC ya fitar a ranar Alhamis da ta gabata, ya buƙaci Shugaba Buhari da ya ja hankalin NBC kan ta dawo ta fuskanci alƙibla yadda ya kamata.

Yana mai cewa, hukumar na neman wuce makaɗi da rawa duk da ba ta hurumi a dimokuraɗiyya.

Don haka ya yi kira ga gwamnati da ta janye dakatarwar da ta yi kana ta yi riƙo da dokokin kundin tsarin mulki na 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima.

Rafsanjani ya yi ra’ayin cewa matakin na NBC “ya fallasa aniyar da gwmnati ke da ita ta neman dagula harkar jarida da kuma daƙile ‘yancin faɗar albarkacin baki da maida Nijeriya ta zamo sai yadda aka yi da ita.