Igboho ya faɗa a komar hukuma

Daga WAKILINMU

Jami’an tsaro sun cafke jagoran fafutIkar ƙwatar wa Yarabawa ‘yanci, Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho.

An cafke Igboho ne jiya Litinin da daddare a Kwatano da ke Tarayyar Benin yayin da yake ƙoƙarin tsallakewa ya bar Afirka.

Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa, Igboho ya bar Nijeriya zuwa Kwatano ne saboda shirin da yake da shi na sulalewa daga Afirka zuwa ƙasar Jamus don tsoron kamun hukuma amma ya zamana haƙarsa ba cim ma ruwa ba.

Ya zuwa haɗa wannan labari, jami’an tsaron da ke riƙe da Igboho na shirye-shiryen dawo da shi Nijeriya.

Idan dai za a iya tunawa, kwanakin baya hukumar tsaro ta DSS ta shiga farautar Igboho ruwa a jallo bayan kuma sun kai samame a gidansa da ke yankin Soka a Ibadan babban birnin jihar Oyo amma ba su same shi ba.