Ilimi da aikin yi ne kadai za su kawar da matsalar tsaro -Yariman Bakura

Daga BASHIR ISAH

Tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura ya bayyana cewar ingantaccen ilimi da samar da aikin yi ga matasan ƙasar nan ne kaɗai zai kawo ƙarshen matsalar tsaro da ake fama da ita.

Sanata Yarima, ya bayyana haka ne a wajen taron goyon baya da Ƙungiyar Matasa Kiristoci ta Najeriya (YOWICAN), ta shirya a ranar Juma’a don mara masa baya kan ƙudurinsa na yin takarar shugaban kasa a 2023.

“Dukkan matsalolin tsaro da suka addabi ƙasar nan na da alaƙa da rashin samar da ingantaccen ilimi ga ‘yan kasa.

“Za mu samar da ilimi kyauta ga duk wani yaro tun daga matakin Firamare har zuwa kammala sakandare, babu yaron da za mu bari ba yare da ya samu ilimi ba,” cewar Yarima.

Kazalika, tsohon gwamnan ya ce da zarar ya dare kujerar shugabancin ƙasar nan zai tabbatar da cewar matasa sun amfani a mulkinsa fiye da kowa.

“Za mu samar da bashi ga matasan da suka kammala karatu don su fara kasuwanci, wanda zai taimaka musu wajen daukar nauyin kansu da wasu.”

Da aka yi wa Sanata Yarima tambaya kan batun bayar da dama ga kowane dan ƙasa wajen yin addininsa, Yarima ya bayyana cewar kundin tsarin mulki ya ba wa kowa damar gudanar da addininsa ba tare sa tsangwama ba.

“Mutane na amfani da adadi wajen raba kan mutane don cimma buƙatar kansu.

“Amma mu za mu ba wa kowa dama, duk mabiya addinin kirista sun san irin damar da muka ba su lokacin da muka mulki Jihar Zamfara.”

Da ya ke nasa jawabin shugaban YOWICAN, reverend Simon Dole, ya ce ƙungiyar ƙarƙashin jagororinta da ke jihohin Arewa 19 da Abuja sun shirya marasa masa baya don zama zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Najeriya a 2023.

“Mai girma Sanata mun san irin rawar da ka taka a Zamfara wajen samar wa Kiristoci aiki da ba su damar yin addini ba tare da tsangwama ba, wannan ya nuna cewar kai shugaba ne na ƙwarai.

“Shugabanni da dama sun shugabanci Najeriya amma har yanzu babu abin da ya sauya, don haka ya kamata mu gwada mutane masu riko da addini,” in ji Dole.

Bayan rufe taron ƙungiyar ta karrama tsohon gwamnan da lambar yabo tare da jadadda goyon bayansu a gare shi.