Ilimin sana’a kafin fara ta na da matuƙar muhimmanci – Hauwa Garba Ilah

“Ba sai ka rasa ba ne za ka yi sana’a”

Daga AISHA ASAS

Yanayin yadda mata matasa ke zage damtse wurin neman na kai don gujewa zaman kashe wando abin a yaba ne, a kuma jinjina wa ƙoƙarin su, ganin cewa, ba su bari ƙalubale da irin kallon da al’ummarsu ke yi masu ya sare masu gwiwa ba. Bincike ya nuna cewa, adadin mata da ke neman na kai a Ƙasar Hausa na gab da cimma adadin da ke zaman banza. Wannan kuwa ba ƙaramin cigaba ne a rayuwar mata, musamman ma bayan aure, kasancewar sana’a na taka muhimmiyar rawa a zamantakewar aure. Da yawa aure na mutuwa sakamakon abin amfani da bai kai ya kawo ba, kamar ashana ko magi, wataƙila hakan ne ya sa matan suka ƙara zage damtse don ganin sun kare kansu da aurensu daga musibar rashi. A wannan sati shafin Gimbiya ya zaqulu wa masu karatunmu wata matashiya da ya kamata mata su jinjina wa, kasancewar ta ɗauko ɗaya daga cikin sana’oun da al’ummar Hausa suka fi dangantawa da maza, ta ce zata iya, ta yi, har kuma ta yi nasarar taka matakin cin moriya. A tattaunawar mun taɓo rayuwa da kuma yadda ta kai ga ƙulla sana’ar da kuma dalilin da ya sa ta sha’awar zavan sana’ar. Idan kun shirya, Aisha Asas ce tare da Hauwa Garba Ilah:

MANHAJA: Masu karatunmu za su so jin tarihinki.

HAUWA: Ni dai sunana Hauwa Garba Ilah, haifaffiyar Jihar Sakkwato, a Sakkwato nake anan na girma. Na yi dukka karatu na a Sakkwato . Ni ɗaliba ce, Ina MSc akan Industrial chemistry.

Mecece sana’arki?

Sana’a ta ita ce, Ina sana’a ta jigilar saƙonni, kaiwa da amsowa na ciki da wajen Sakkwato, wato ‘delivery services’ a turance, kuma na sa wa kamfanin nawa Hech’s Courier Service. Muna aiki a tsakanin Sakkwato da Kebbi. Baya ga haka, na kasance ‘yar kasuwa da ke sana’ar siyar da jakukuna da kuma takalma.

Me ya sa ki tunanin zaɓar wannan sana’a?

To ita dai sana’ar kai saƙo, wato ‘delivery services’, ta samo asali ne kan irin ƙalubalen da nake fuskanta idan na zo aika kayan da nake sayarwa ga waɗanda suka siya. Sau da yawa sai da ƙyar nake samun wanda zai kai min kayan, ko amso min wani saƙon na daban, da wannan ne na fara tunanin sana’ar ta kai saqo, duba da cewa, sana’ar ba ta yawaita ba anan Jihar Sakkwato , Ina magana akan shekarar 2021. To daga nan ne na yi tunanin fara wannan sana’a don sawwaqa wa kaina da kuma samun ƙarin sana’a wadda na yi hasashen za a samu alfano a cikinta.

Ko kin fuskanci wata matsala lokacin da ki ka zaɓi wannan sana’a a matsayin ki ta mace?

Alhamdu lillah. Gaskiya ba zan ce na fuskanci wata matsala sosai ba, kasancewar na samu goyon bayan iyaye da abokanaina. Ko kaɗan ba su sare min gwiwa ba.

Ba mu labarin irin matsalolin da ki ke fuskanta a wannan sana’a?

Matsala ta farko dai farawa ba tare da cikakken ilimi kan sana’ar ba. Kasancewar komai za ka yi sanin sa kafin aikatawa na da muhimmanci. Ƙwarai yake da muhimmanci samun ilimin sana’a kafin ka fara ta. Wannan ce ta kasance domin na fara cikin duhun kai, kuma ban san kowa da ke irin sana’ar ba. Don haka aka haɗu da ‘yan matsaloli.

Sai kuma matsala ta biyu, ban san mutane sosai ba, kuma ban cika hulɗa da mutane ba, don haka ban iya mu’amala da su ba, wanda sai a hankali na iya kuma na saba da irin sha’anin jama’a.

Baya ga haka, na ɗan samu ‘yar matsala da yadda zan juya akalar sana’ar da ma ma’aikatan da ke aiki a ƙarƙashina. Kuma kafin ma in samu waɗanda za su yi aikin ma sai da aka ɗan samu matsala kasancewar sana’ar baƙuwa a lokacin.

Za mu so jin nasarorin da ki ka samu.

Alhamdu lillah! Akwai nasarori da dama da na samu, wanda zan ce sai dai godiya. Sana’a na ta ƙara albarka, duba da cewa, an faro ba da wani abu sosai ba, amma cikin shekaru biyu mun yi nasarar zama ɗaya daga cikin farko-farko idan ma ba mu zama na farko ba a manyan ‘delivery companys’ da aka sani kuma ake son amfani da su a Jihar Sakkwato. Duk da cewa ban kai inda nake fatan kai wa ba har yanzu, amma alhamdu lillah an samu nasara mai tarin yawa. Kuma na san da addu’a da kuma dagewa, za mu kai inda muke fatan zuwa.

A taki fahimta menene matsayin sana’a ga ‘ya mace?

Sana’a ga mace wata muhimmiyar abu ce, da ba za a iya ƙayyade alfanun ta cikin ƙaramin rubutu ba. Kuma wani abu mai matuƙar muhimmanci da ya kamata mu fahimta game da sana’a shi ne, ba wai sai ka rasa abu ka ke sana’a ba, a’a. Dogaro da kai na da amfani, yau ace za ki iya yi wa kanki abinda ki ke so har ki taimaka wa wani ba tare da kowa ya sani ba. Gaskiya abin akwai daɗi.

Bari mu koma vangaren iyali. Akwai ko babu?

(Dariya) ba ni da aure, bare a kai ga samun yara.

Menene bambancin mace mai sana’a da kuma mai zaman banza?

Akwai bambanci sosai, ba ma za a haɗa ba. Wadda ba ta da sana’a ba ta da hanyar mayar da Tarau Sisi, Ina maganar idan an cire mai aikin gwamnati. Wanda hakan na nufin kalar shigarta ma daban ta ke.

Ita sana’a komai ƙanƙantar ta tana tasiri, domin dai ba a zama ba na ɓatarwa. Ita kuwa wadda ba ta da sana’a sai kallo, dukkan buqatunta sai ta yi ‘yar murya ta ke samun yin su. Kuma a wurin marar aikin yi ce ake tarar da gulma da ƙananin maganganu. Saboda ba ta da abin yi, don haka rayuwar wasu ta zama abin kallo gare ta.

Duk wani abu da ɗan Adam ke yi yana da inda yake fatan isa. Menene burinki ta fuskar sana’ar da ki ke yi?

Babban burina shi ne, a ce yau Hech’s courier service ya karaɗe Nijeriya, ya zamo ba inda za ka bulace mu da ba ma aiki a can.

Ko sana’a na hana karatu?


Sana’a ba ta hana karatu, sai dai idan ka ƙudiri aniyar yin hakan dole sai ka jajirce, kasancewar tauna taura biyu a lokaci ɗaya zai ɗan yi wahala.

Wacce matsala ce ku ka fi fuskanta daga wurin kostamomin ku?

Matsalar ‘customers’ marasa haƙuri, da masu zagin ma’aika ta. Nasan mukan sava masu, mu yi ba dai dai ba, amma akan yi uzuri. Aikin nan kowa fa a lokacin da ya yi kira yake so a yi hanzarin cika masa buƙatar tasa, sai dai abinda suke mantawa ba kullum hakan zata iya samuwa ba, kasancewar ba kullum ne za ka tarar da masu kai salon a zaune ba, wani lokacin sun tafi cika bulatar wasu, tunda abu ne na jama’a da yawa. Wannan kan sa wasu gajin haƙuri, su kai ga faɗa.

Sau da yawa za ki tarar da cewa mutane musamman ma a Ƙasar Hausa suna bambanta sana’ar mace da ta namiji. Shin kin samu lalubale a wannan vangare?

Zan iya cewa ban samu ba, duba da cewa ba wanda yake min irin maganar, amma dai mutane na danganta sana’ar da sana’ar maza ba mata ba.

Wane kira za ki yi ga mata matasa kan ba wa sana’a muhimmanci?

Shawara ta ga mata, ita ce, su damƙi sana’a. Ko kuna da arziki ko ba ku da ku yi sana’a, domin ita sana’a tana da amfani sosai. Aikin gwamnati nada wahalar samu, don haka yake da muhimmanci koyo da riqo da sana’a tun daga ɗalibai, zuwa waɗanda suka gama, da kuma waɗanda ba su yi karatu ba. Kai har ma waɗanda suka yi sa’ar samun aikin na gwamnati ya kamata su riqe sana’a don lokacin ritaya da kuma matsala da ba a so. Idan aka jajirce kuma ana addu’a, sai kaga an samu rufin asiri.

Ta yaya ki ke iya jan ragamar sana’arki kasancewar maza sun fi yawa a waɗanda ke yi ma ki aiki?

Kusan zan iya cewa daga zuciya ce, domin duk abinda ka sa wa ranka kana so, za ka iya yin shi, to fa duk wata matsala mai sauƙi ce, don za ka iya lalubo maganinta ba tare da ka yi fushi ko ka nuna gajiyawa ba. Ba abinda zan ce dai godiya ga Allah.

Na gode.

Ni ma na gode ƙwarai da gaske.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *