Illar fyaɗe

Fyade

Daga AISHA ASAS

Masu karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin iyali na jaridar Manhaja, fatan Allah Ya albarkanci zuri’armu, Ya ba mu zaman lafiya.

Kafin komai zan so mu fara da bayyana ma’anar kalmar fyaɗe kafin mu kai ga tattauna matsalolin da ake fuskata bayan fyaɗen.

Fyaɗe wani nau’in cin zarafi ne ta ɓangaren jima’i, amfani da ƙarfi yayin kusantar mace ko namiji, ma’ana yi ba da amincewar abokin tarayya ba.

Idan aka ce fyaɗe, hankalin mutane ya fi tafiya ne ga mata, a ganin su mata ne kawai ake yi wa cin zarafi ta ɓangaren fyaɗe. Ko kaɗan wannan zance ba haka yake ba, domin an tabbatar kaso 29 bisa ɗari na mazan duniya sun fuskanci cin zarafi ta vangaren fyaɗe.

Hakan ba yana nufin adadin matan da ake yi wa fyaɗe na daidai da na maza ba, domin na matan ya linka na mazan har da ɗori, dalilin kenan da ke sa ake ganin kamar mata ne kawai wannan musiba ke hawa kansu.

Bincike ya nuna cewa, yara ƙanana mata ne suka fi yawa a matan da aka fi yi wa fyaɗe, yayin da manyan mata daga wuraren aiki kan samu wannan cin zarafi daga mazan da suke ƙarƙashin su a wurin aiki, sai kuma mata a masana’antun finafinai na duniya, kamar yadda a kwanaki da yawansu suka yaye labule kan irin fyaɗen da aka yi masu kafin kawowa matsayin da suke.

Haka ma za a iya samun kaso mai nauyi daga matan da suke gidajensu, wasu ta sanadin dirar ‘yan fashi a gidan, ko kwarto, ta hannun ‘yan’uwansu, ko kuma idan sun fita zuwa wani sha’ani.

Abin takaici da tashin hankali game da wannan musiba ta fyaɗe, yadda har iyaye ake samu da aikata fyaɗe ga ‘ya’yan da suka haifa da cikinsu.

Kamar yadda wani bincike da wata jaridar a nan gida Nijeriya ta yi, ta tabbatar iyaye 34 suka yiwa ‘ya’yan cikinsu 48 fyaɗe a shekaru biyu da suka gabata, kuma adadin ya samu ne a jihohin 13 daga jihohin da muke da su.

Abin ƙarin tashin hankali kuwa, mafi rinjayi na daga wannan adadi ƙananan yara ne kuma mata, har da ‘yar watanni 15 da haihuwa, namiji ɗaya ne a wannan lissafin, yayin da aka samu manyan mata huɗu.

A taƙaice dai abin nufi babu inda mace za ta shiga ta ɓuya daga cin zarafi na fyaɗe, sai ga wadda Allah Ya kare.

Wasu masana sun bayyana fyaɗe a matsayin wani nau’i na matsalar ƙwaƙwalwa, domin ga wasu ko ga matansu ba sa samun gamsuwa matuƙar ba ta ƙarfi suka yi masu ba. A wani vangare fyaɗe ga wasu tsabar rashin imani ne ko biyayya ga ƙwaya, ko neman duniya da zai sa ka karɓi ɗabi’ar a matsayin sharaɗi daga boka.

Bincike ya nuna, kaso mai yawa na mata musamman ƙananan yara daga Arewacin Nijeriya sun fuskanci wannan cin zarafi na fyaɗe, sai dai da yawa daga ciki iyaye ko su karan kansu yaran na yin gum da bakinsu don gujewa rasa mijin aure, ko irin kallon da al’ummarsu za su yi masu.

Da wannan ne muke so mu gina darasin namu na yau, domin illar fyaɗe ta fara ne daga lokacin da aka yi zuwa matakin da za a ɗauka.

Masana ƙwaƙwalwa sun tabbatar da cewa, fyaɗe ba iya al’aura illar sa ke tsayawa ba, asali ma idan da kulawa, akwai yiwar a iya kawar da matsalar ta wannan wuri cikin lokaci, (ga manyan mata, yayin da a ɓangaren ƙananan yara ya danganta da irin damejin da aka yi masu) sai dai matsalar tana tuma ne ta tava ƙwaƙwalwa, wannan zai sa tabon ya ɗauki shekaru bai gushe ba, kuma zai iya tasirin haifar da wata nau’in taɓin hankali, wanda za su iya samun kansu a tsoron mu’amala irin wannan ko su dinga ganin za a yi masu ta ƙarfi ne, har su kai ga ƙoƙarin illata abokin mu’amala tasu, a ganin su kare kansu suke yi.

Ta yaya fyaɗe ke samun damar yin wannan illar?

A yayin da aka yi wa ‘yarki ko ɗanki fyaɗe, abu na farko da suke buƙata shine, kai su asibiti don tabbatar da irin lahanin da aka yi masu, da kuma ba su taimakon da ya dace.

Idan an samu wannan, mataki na gaba da wanda aka yi wa fyaɗe ke buƙata shine, samun wanda za su sanar da shi abinda suke ji, kuma babu wadda ta cancanci wannan matsayi sai ke uwa. Ki ba wa ‘ya’yanki damar fayyace abin da suke ji da kuma yadda suke so a yi game da wanda ya keta masu rigar mutunci. Koda kuwa ƙananan yara ne, ki ba su dama, domin hakan ma zai sasu amayyar da ƙuncin su, wanda zai rage masu nauyi a zuciya.

Mataki na gaba, bin hanyar da ta dace don ƙwatar masu haqqin cin zarafin da aka yi masu. Masana sun ce, hukunta wanda ya aikata fyaɗe na ɗaya daga cikin magungunan da ke samar da warakar zuci ga wanda aka yi wa fyaɗen. Sanin wanda ya aikata masu wannan tu’annati ya ɗanɗana kuɗar sa zai rage masu raɗaɗin a duk lokacin da suka tuna.

Ganin wanda ya yi masu fyaɗe na walwala da rayuwa cikin jin daɗi kawai zai iya hana wadda aka yi wa sakewa. Wannan kuwa kan samu bisa dalilai biyu, ko dai iyayen sun yi shiru don ba su so a san an yi wa ‘yarsu fyaɗe, wanda hakan zai ba wa mai fyaɗen damar yin rayuwa tamkar bai aikata hakan ba. Ko kuma yanayin gurɓacewar ɓangaren shari’a, ba wa mai laifi gaskiya don matsayi ko kuɗin da yake da su.

Duk da cewa, wasu lokuta ba a sanin ko alƙalin zai yi adalci, dalilin voye lamarin da iyaye ke yi, sakamakon gudun irin kallon da za a dinga yi masu, ko kuma yarinyar ta kasa samun mijin aure.

Wannna matsala na ɗaya daga cikin rashin adalci da al’umma ke yi wa matan da aka ci zarafin su ta fuskar fyaɗe, musamman ma a Ƙasar Hausa. Da yawa akan nuna ƙyama maimakon tausayi ga macen da aka keta wa rigar mutunci, kuma hakan kan faru ne da masaniyar ba laifinta ba ne.

Idan aka yi wa yarinya fyaɗe, kuma mutane suka sani, maimakon a taru a zame mata ƙarfen da zai ƙarfafa mata zuciya, a bata kulawa, a haxa kai wurin ƙwatar mata haƙƙinta, a’a, kawai za ta zama darasin tusawa a duk lokacin da aka haɗu majalisa, za ta zama abin nunawa a duk sa’ilin da ta wuce, zata zama abin ƙyama a yayin da aka yi zancen mai auren ta.

Da wannan ne za ka tarar a unguwa ɗaya an samu mutum ɗaya ya yi wa yara goma fyaɗe, kuma yana zaune abunsa ba tsangwama bare kora, asalima ko uban yarinyar ba shi da halin faɗa da shi ko da na fatar baki ne. Dalili yana gudun a tambaye abinda ya haɗa su, har ta kai ga a fahimci fyaɗe ya yi wa ‘yarsa.

Idan da al’umma za su cire kyama, su mayar da tausayi a gurbin ga wadda aka ci zarafin ta, da ya taimaka matuƙa wurin rage yawaitar masu fyaɗe musamman a Ƙasar Hausa, saboda ta hakan ne kawai za a iya ba wa iyayen wadda aka yi wa fyaɗe damar ɗaukar mataki.

Akwai al’umma a can cikin ƙasashen ƙetare da na taɓa jin labarin cewa, sun nemi dama daga hukuma kan a amince a ba wa kowane mai jagorancin ƙauyen damar iya yanke hukuncin fyaɗe idan an kawo masa. Da wannan aka ce, idan aka kama wani da laifin fyaɗe, bayan an tabbatar, za a karve wani kaso mai yawa na abinda ya mallaka a ba wa yarinyar da ya yi wa fyaɗe, sannan a yi masa dadaƙƙa, kafin samarin garin su zaga da shi lungu da saƙon garin don nuna shi a matsayin wanda ya yi fyaɗe, aka hukunta shi, hakan zai hana shi samun matar aure, idan yana da aure, matarshi na da zaɓi na barin shi ta auri wani.

Mu ƙaddarta cewa, a al’ummarmu ake wannan hukunci, kuma ana yin adalci yayin hukunta talaka da mai kuɗi duk ɗaya ne matuqar ka aikata laifin za ka fuskanci irin wannan hukunci, ba na tunanin za a kai wannan lokacin ba a rufe babin fyaɗe a tsakaninmu ba.

Kowa na da rawar da zai iya takawa ga rayuwar macen da aka yi wa fyaɗe, tun daga iyaye ta hanyar bata kulawar da ta dace kamar yadda muka faɗa a baya, al’umma su daina qyama da bambanta ta da sauran mata, su daina gudun auren wadda aka yi wa fyaɗe, su haɗa kai wurin ganin an ƙwatar mata haƙƙinta ko da hakan na nufin korar wanda ya yi fyaxen daga cikin su, ko ba ku yi don Allah ba, ku yi don yayyafa wa gemunku ruwa yayin da na ɗan’uwanku ya kama da wuta.

Idan aka kasa samar da waɗannan matakai ga macen da aka yi wa fyaɗe, akwai yiwar ta taso da matsala a jikinta, wadda sai ta yi aure ne mijin ko ita za su iya fahimtar tana da ita, sakamakon rashin duba wurin a lokacin da aka yi fyaɗen, ko kuma ta rasa sha’awar namiji gabaɗaya ta yadda sai da dole mijinta zai kusance ta, wani sa’in ma zata iya samun matsalar tsoron kusantar har a fara tunanin mutanen ɓoye ne suke tare da ita, sakamakon kai wa mijinta hari da ta ke yi a duk lokacin da ya yi yunƙurin kusanto ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *