Illar rashin ɗaukar nauyin ’ya’ya

Daga SADIYA GARBA YAKASAI

Yau ma ga mu a filinku mai albarka na Tarbiyya a shafin jaridarku ta Manhaja, inda kamar yadda mu ka saba, za mu ɗora daga inda muka tsaya. Da fatan ku na biye da mu kamar kullum.

Mun ɗan samu ƙorafin mata a kan maza masu fita ba tare da sun wadata gidansu da abubuwan buƙata na rayuwa ba. Amma su suna fita su biya wa kansu buƙatarsu ba tare da sun tuna iyalinsu na buƙatar kulawarsu ba.

A ce maza ba za su ba da kuɗin cefane yadda ya kamata ba, sai su fita su bar ma ta da yara. Idan an ci sa’a ne, wasu ke ɗaukar wani abu su ba wa matan, shi ma ba ishasshe ba. Wannan ba daidai ba ne. Idan ka ƙi ba da cefane da abun dafawa, ka bar matarka ta nema ta dafa ba tare da ka duba a ina za ta samu ba, wannan rashin adalci ne, kuma ƙuntata ce. Hakan kuma yana gwada wa mace ta nema ko ma a ina ne baruwanka. mata da yawa na kuka kan wannan baƙin mulkin mallakar da maza ke yi mu su.

Yana da kyau ka duba, kai ka ce ka ji ka gani za ka iya da nauyinta, da na yaranka. Saboda Allah idan ba ka ba da ba, ina za ta samo? Sai dai idan sana’a take, ko aiki. amma idan ba wannan, to ka sa a ranka ka ci amanar da Allah ya ɗora ma.

Wasu mazan kuma sai su ba da abu kaɗan su ce da mace a cika a yi raba-daidai, wai ita ma ai yaranta ne ba shi kaɗai ba.

Bai yi tunanin ita ma da shi ta karu ba. Idan bai ba ta ba, to ina kenan za ta samu? Kuma ya tsare fuska da muzurai don ma kar ta kawo masa dalilanta. Cefane ma kenan namiji ya gudu, ina kuma ga sauran buƙatun rayuwa?.

Ta yaya namiji zai sakar wa mace nauyin gidansa kuma ya ce zai ga dai-dai? Wasu da yawa wannan ɗabi’ar ce ke ruguza musu gida. Iyaye mata su zamo kamar taɓaɓɓu saboda tunani yaya za su yi, su wadata yaransu. Ko ya hana na rana ka ba da na dare. To ranar dole yara ko su damu uwa ta ba su don ita ce a tare da su, kuma ita suka ɗora wa damuwarsu.

Wannan rayuwan da muke ciki ta canza. wasu mazan da yawa wallahi ƙiri-miri suke nuna muguntarsu ga matansu. Wasu ƙyashi ke sa wa su ƙi yi wa matansu komai. Sai su wayance wai tana sana’a ko tana aiki tana ɗaukar albashi. saboda haka a wajensa, ita ma dole ta ba da.Ya manta kafin ta ci naira ɗari cikin kuɗin yaransa sun ci dubu.

Ba wai mace kar ta taimaka wa mijin ta ba. Idan tana da shi don ta yi ba laifi ba ne, duk taimakon kai ne. Amma ya ce lallai sai ta yi shi ne ba dai-dai ba. Ruwanta ne ta taimaka, ruwanta ne ta ƙi. Kai dai ya zame maka dole sai ka yi iya iyawar ka ba tare da ka sawa kanka wahala ba.

Wani namijin ba babu ce ke hana shi bayarwa ba. Kawai tsabar ƙeta ce. Amma shi zai fita ya ci a waje, ya ƙoshi. Ya manta da iyalinsa da ya hana ko ya ba su kaɗan. Shi kuma ya samu gidan abinci ya baje kolinsa, Shi ga mai ku]i. wani abincin ma na wajen bai kai darajar na gidanka ba.

Wannan ɗabi’ar ta zame wa maza jinin jikinsu. Mata na kuka sosai da wannan rashin adalci da suke musu. Yana da kyau maza su farka daga ɗumammen baccin da suke gaskiya, in mu ne yau, gobe fa?

Wannan hali ke sa wasu yaran shiga kwaɗayi wallahi. Saboda a gidansu ba a ba su sun ci sun koshi ba. Kuma sun shiga wani gidan sun ga cima ba irin tasu ba. Shikenan da rana tsaka an koya wa yara kwaɗayi da bin gidaje.

Gyara waje ba ka gyara gida ba; Ma’ana za ka ga mutum ya fita gidansa bai ajiye ba, kuma bai damu da halin da iyalinsa za su shi ga ba. Amma abun mamaki zai iya yi wa mutane abokansa ko wasu ya yi musu bajinta. Sai ya kai su gidan cin abinci lafiyayye, ya kashe musu kuɗi. Amma gidansa a ce ya ba da kuɗin cefane, bai fi ya ba da ɗari uku ba ko dari biyar. Wasu gidajen ma, ba sa kai wa haka. Shi ne wai kuɗin abincin gidansa. Idan ya ga dama ciki zai ce a yi awo, a kuma sai kayan miya. Ƙarin ƙarfin hali ya ce har ita ce da su Magi a wannan kuɗin.

Don Allah ina haka za ta faru? Sai ma idan ya dawo, sai ya ce wai ina abincinsa? A fa wannan kuɗin da ya ba da. Idan an ce babu, zai rufe matar da faɗa har da su habaici duk zai iya yi. Ya ce ya ba da kuɗin cefane amma an ƙi ajiye masa.

Shi ya sa mata da yawa suke shiga matsalar bashi. Abinci bai kai ba, ga kudin sabulu wanka ko na wanki, man shafawa da sauran abubuwa na rayuwa ba su wadata gidan ba. Kuma dole suna buƙata, amma babu. Dole ko mata su fita cin bashi.

Mu gangara kan batun yaranmu mata da iyaye ne ke da alhakin kula da duk wasu bukatunsu. Amma iyaye sun yi wa abun rikon sakainar ɗiban kashi. Akwai abubuwan da ya kamata a ce iyaye ne ke sayawa yaransu na amfanin kansu, amma sai iyaye su ɗauke kai. Su kuma yara sai su ɗora buƙatunsu a kan samari wanda hakan ba dai-dai ba ne, ɓata tarbiyya ne.

Yadda zamanin nan ya koma sai fa duk mun taru mun sa wa yara ido. Alhakin iyaye maza ne su duba duk wasu buƙatar yaransu mata. Don gujewar faruwar abubuwa marasa da]i. Wannan bayani ne mai zaman kansa sati mai zuwa zamu faɗaɗa shi mu ga abunda za mu iya.

Sannan su ma mata a rage burin sai an ci mai kyau. Yanzu zamani ya canza. Abunda za ka saya dubu ɗaya, sai ka saya dubu ɗari biyu. To idan kuma iyali suna da yawa, dole kuɗi ya yi yawa. Shi ya sa maza ke ƙorafin kuɗin cefane,5 dai-dai ruwa, dai-dai ƙurji, haka rayuwar yau ta koma. Wani ma idan ya ci na safe ba ya samun na rana. Wani kuma har daren ma babu. Wannan hali ne na rayuwa da muka samu kanmu sai dai addu’ar Allah ya yafe mana ya kuma ba wa kowa yadda zai yi.

Mazaje a yi haƙuri a dinga kamanta adalci. Ba lallai sai an yi mai tsada ba. A yi dai ko garau-garau ne, amma mai daɗi, yadda iyalinka ba za su yi kuka da kai ba.

Mu kuma mata, mu zaunar da yaramu, mu karanta musu yadda rayuwa ta canza ne ya sa ba sa ganin abunda suke so. Don Allah iyaye mu dinga tausar yaranmu da kalamai masu daɗi, yadda ba za su zargi mahaifinsu da yana takura musu ba. Ko ba ya ba su, ko da kuwa hakan ne, bai kamata yara su fuskanci halin da suke ciki ba. Don shi yaro bai da mantuwa.

Allah sa mu dace mu gane mu gyara Allah kowa ya hore masa yadda zai yi a gidansa. Mu tara cikin sati mai zuwa. kofa a buɗe take kullum gyara ko shawara, ko neman shawara duk muna maraba a jaridarmu ta MANHAJA.

Wassalam.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *