Illolin shaye-shayen ƙwayoyi da hanyoyin shawo kan lamarin

Shaye-shaye ya zama ruwan dare a tsakanin al’umma musamman ma matasa maza, wanda babban abin takaici halayya ce da aka fi dangantawa ga maza, sai ga shi ta zama ruwan dare har mata sun fi maza iyawa. Masu aure da waɗanda ba su da shi, shaye-shaye na nufin duk wani yanayin da ɗan adam zai saka kan shi don sauya yanayin tunaninsa ko nazarin shi ta yadda ba zai iya bambanta ya kamata da akasin hakan ba.

A zamanin baya, muna jin labarin irin waɗannan ɗabi’un a ƙasashen ƙetare, wasa-wasa har ta shigo cikin ƙasarmu da al’ummarmu.

Da yawa mutane ba su san me ke kawo wannan ɗabi’ar ta shaye-shaye ba, ko kuma suna kan hanyar faɗawa shaye-shayen ba tare da sun sani ba.

Shaye-shaye na zuwa ne a yayin da mutum ya afka cikin shan kwaya saɓanin yadda aka ƙayyade a sha shi, ko kuma shan giya ko tabar wiwi da dai sauran nau’ukansu waɗanda za su bugar da mutum ko su kai shi ga maye.

Wasu daga cikin nau’ukan shaye-shaye:

  • Shan maganin da doka ya hana amfani da shi.
  • Shan magani barkatai, ba tare da izinin likita ba.
  • Wuce umurnin likita wajen shan ƙqwayoyi
  • Shan giya da duk wani abin da zai bugar da mutum.

Wasu daga cikin dalilan da ke saka shaye-shaye su ne; jahilci, matsalolin rayuwa, al’adu, hulɗa da abokan banza, sakacin iyaye, yanayin wurin zama, aikin ƙarfi, samun ƙwayoyin cikin sauƙi da dai sauransu.

Wasu daga cikin miyagun ƙwayoyi da aka fi amfani da su wajen shaye-shaye su ne; biyo bayan shan giya da tabar wiwi da sholishon da hodar ibilis wajen buguwa ko maye, mashaya har ila yau, na amfani da wasu ƙwayoyi don buguwa waɗanda
suka haxa da; Valium tabs, D5 tabs, Diazepam, tabs, Exol 5 tabs, Tramadol tabs, Pemoline tabs, Emzolyn expectorant, Tutolin, expectorant, Codeine syrup, Benalyn syrup, Pacaline syrup, Pento injection, Legatine injection.

Wasu daga cikin matakan shaye-shaye:

  • Matakin farawa ko gwaji; wannan shi ne mataki na farko wanda mutum zai soma kusantar ko soma mu’amala da masu shaye-shaye har ta kai shi ga soma tavawa kaɗan.
  • Shaye-shaye a matakin ganin dama:- Wannan matakin mai shaye-shayen yana sha ne lokacin da ya ga dama, ba ya saya da kuɗinsa, sai an samu na banza ko na bati.
  • Matakin shaye-shaye ba ƙaƙƙautawa; wannan shi ne matakin kama shaye-shaye gadan-gadan, ko da kuɗi ko babu sai an sha.
  • Matakin dogaro da shaye-shaye; wanda ya kai wannan matakin to lallai ba zai iya komai ba sai ya sha idan bai sha ba kuwa ba ba zai iya zama lafiya ba, wanda ya kai wannan matakin kullum za ka same shi ko same ta cikin maye, a wannan matakin ana iya sata domin a sayi kayan mayen.

Wasu daga cikin illolin shaye-shaye;

Biyo bayan kawo rashin karvuwa a wurin mutanen arziki da zubar da mutunci, shaye-shaye kan janyo: Talauci da jahilci, Ciwon huhu, ciwon hauka, ciwon hanta, ciwon kansa.

Ciwon suga, ciwon sanyin kashi, ciwon sankarar mama, yawan tunani mai tsanani da muni wanda zai kai ga ciwon hawan jini da zuciya, yana kawo lalacewar mazaƙuta, yana kawo lalaci, yadda mai shaye shaye baya iyayin komai sai ya sha.

Illar shaye-shaye ga al’umma shi ne idan mutum ya riski kansa a yanayin shaye-shaye, haƙiƙa rayuwarsa tana canjawa gaba ɗaya.

Abin zai tava lafiyarsa da mu’amalarsa da mutane. Aikinsa kai har hankalinsa zai iya rasawa baki ɗaya ko a wayi gari mutum ya rasa ransa, to mene ne ribar hakan?

A cikin al’umma duk wata ɓarna, ta’addanci da rashin sa ido za ka ga sun faru sai ka tarar da mai aikata wannan abin yana da ɗabi’ar shaye-shaye. Misali ’yan fashi masu yi wa mata fyaɗe, manya da ƙananun ɓarayi.

Shaye-shaye na kawo mutuwar aure da rasa aikin yi da talauci da rashin zama lafiya da mutane da taɓarɓarewar tarbiyar yara da faɗace-faɗace.

Ashe wannan zai nuna mana cewar matsalar shaye-shaye ba ƙaramar matsala ba ce ga rayuwar mutum da al’umma baki ɗaya.

A mahangar wannan jaridar, bayan huvvasar gwamnati a matakai daban-daban wajen hana fasa-ƙwarin ƙwayoyin, har ila yau ya zama dole iyaye su tashi tsaye wurin kula da tarbiyyar ’ya’yansu da matasa, sannan su riqa kula da harkokin ’ya’yansu na yau da kullum, su kuma kula da irin abokan da yaransu suke hulɗa da su. Dole ne sarakuna da malaman addinai su ma su tashi tsaye wurin tsawatarwa da faɗakar da al’umma bisa illar shaye-shaye ta mahangar addini da rayuwa. Dole ne kuma al’umma su ba da haɗin kai wurin taimaka wa jami’an tsaro da Jami’an Yaƙi Da Fatauci Da Shan Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa wurin gudanar da ayyukansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *