Daga AMINA YUSUF ALI
Wakili daga Gidauniyar Kudi ta Ƙasa da Ƙasa (IMF) a ofishinsu na Nijeriya, Ari Aisen, ya bayyana cewa, ya kamata Nijeriya ta san yadda za ta tsara yadda take kashe kuɗinta in dai har tana son ta warware matsalolin bashin da take ciki.
Aisen ya bayyana haka ne a yayin sha’anin da Talabijin ɗin yanar gizo ta Proshare WebTV ta shirya a kwanan nan.
A cikin jawabin nasa ya yi kira ga ofishin kula da bashin (DMO) a kan buƙatar Nijeriya ta duba al’amarin rashin kuɗin shiga da ake fama da shi.
A cewar Aisen, “Ofishin DMO yana iya ƙoƙarinsa a fannin ɗaukar nauyin kashe-kashen kuɗin da gwamnati take buƙata. Amma abin a bayyane yake, in dai har ana son a warware matsalar bashi a Nijeriya, dole a mai da hankali a kan kuɗin shiga da yadda ake kashe kuɗi”. Inji shi.
Ya ƙara da cewa, kashe kuɗaɗe mafi yawa daga kuɗin shiga ɗan kaɗan da ake samu a Nijeriya yana matuƙar ba da gudunmawa ga ƙaruwar bashin da ƙasar take ciyowa.
Domin a cewar sa, Nijeriya tana kashe sama da kuɗaɗen shigar da take samu.
Sannan kuma ya ba da shawarar da a ƙayyade kuɗaɗen da ake kashewa wanda a cewar sa ita ce babbar hanyar da za ta rage ƙazamin kashe kuɗi kuma ya magance halin nauyin bashin da yake kan Nijeriya a halin yanzu.
A cewar sa, ƙayyade kashe kuɗin abin buƙata ne a kowanne gida. Ba zai yiwu a ce an dawwama kashe sama da abinda ake samu a kuɗaɗen shiga ba.
Don haka, dole ƙasa ta dogara ka’in da na’in a kan kuɗin shigarta kaɗai don ɗaukar nauyin dukka buƙatunta.
Daga nan wakilin na IMF ya yi kira ga Ƙasar Nijeriya da ta mai da hankalin kashe kuɗinta a kan ɗaga darajar rayuwar ‘yan Nijeriya da walwalarsu, ababen more rayuwa, da kuma kauce wa abubuwan da ba su zama dole ba.
Amma a cewar sa, maganar kuɗin shiga tana da matuƙar muhimmanci ga Nijeriya. Domin ana buƙatarsa don samar da ababen more rayuwa, sannan kuma a wani ɓangaren ana buƙatarsa don a samu kuɗi ba sai an nema ba a Babban banki ba.
Don haka a cewar sa, dole sai da kuɗin shigar za a samu damar ɗaga darajar rayuwa, a rage faɗuwar tattalin arziki, wanda zai kawo cigaba, ya samar da abin yi, ababen more rayuwa, inganta harkar lafiya, ilimi, da tsaro, da sauransu.
A cewar sa su ne manyan ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta a yanzu.
Daga ƙarshe, Aisen ya ba da shawara a kan cewa, hakan ba zai tabbata na sai an gudanar da mulki cikin adalci da sanin ya kamata sannan a tafiyar da harkar haraji yadda ya dace inda kowanne vangare zai dinga biyan haraji sannan kuma a dinga ganin tasirin harajin ƙuru-quru a cigaban ƙasa.
Kuma a cewar sa, samun haɗin kan kamfanoni wajen biyan harajin yana daga tafiyar da tsarin mulki yadda ya kamata da kuma yadda gwamnati ta yi amfani da su yadda ya dace. Kuma a tabbatar da kowa da kowa yana biyan harajin shi zai sa a samu nasarar al’amarin.