Imo: Kotu ta umurci INEC ta tabbatar da Ararume a matsayin wanda ya lashe zaɓen maye gurbi

Daga WAKILINMU

Wata Babbar Kotu a Abuja, ta umurci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta bayyana Chief Ifeanyi Ararume a matsayin wanda ya lashe zaɓen maye gurbi na mazaɓar Imo ta Arewa wanda aka gudanar ran 5, Disamb, 2020 a jihar Imo.

Alƙali Taiwo Oladipupo Taiwo shi ne wanda ya yanke wannan hukunci inda ya ce kotu ta hanzarta ta tabbatar da Ararume na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen da aka gudanar.

Kazalika, alƙalin ya bai wa INEC odar ta miƙa wa Ararume takardar shaidar lashe zaɓe cikin sa’o’i 72 daga lokacin da aka yanke hukuncin domin bada damar Shugaban Majalisar Dattawa ya rantsar da shi.

Alƙali Taiwo ya kore wani ƙorafi da APC tare da wani Chukwuma Francis Ibezim suka shigar suna ƙalubalantar kotun ba ta da hurumin sauraren shari’ar Ararume.

Kotun ta ce ƙorafin nasu ba shi da wata daraja saboda shi Ibezim da aka ce ɗan takarar jam’iyyar APC ne a zaɓen maye gurbin, wata Babbar Kotu ta rigaya ta sauke cancantar takararsa, haka ma kotun ɗaukaka ƙara saboda bayanan ƙarya da ya gabatar wa INEC don ya samu shiga takarar.

Lauyan Ararume, Ahmed Raji (SAN), ya shaida wa kotu cewa Ibezim ba shi da hurumin tsayawa takarar a zaɓen maye gurbin tun da tun farko wata babbar kotu da kuma kotun ɗaukaka ƙara sun janye cancantarsa na tsayawa takara.