Imo: Magidanci ya faɗa a komar ‘yan sanda bayan da ya yi yunƙurin halaka ɗan maƙwabcinsa don tsafi

Daga BASHIR ISAH

Wani magidanci mai suna Mr Francis Chukwura, ya faɗa a komar yan sandan jihar Imo bisa zargin yunƙurin halaka ɗan maƙwabcinsa don neman cika muradinsa na tsafi.

Tuni dai wannan al’amari ya yi silar Chukwura ya rasa aikinsa a inda yake aiki, wato FMC Owerri.

Cikin sanarwar da ya raba wa manema labarai a Alhamis da ta gabata dangane da kamun wanda ake zargin, mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Imo, CSP Mike Abattam, ya ce wanda ake zargin ya yaudari Henry Ekwos, ɗan shekara 14, zuwa ɗakinsa inda ya yi yunƙurin kashe shi bayan kuma ya gina wani rami a cikin ɗakinsa kafin daga bisani asirinsa ya tonu aka ceto yaron.

A cewar sanarwar, “Lamarin ya auku ne a Ubommiri da ke yankin ƙaramar hukumar Mbaitoli a jihar Imo, a ranar 06/01/2022 inda wani Francis Chukwura ya yaudari ɗan maƙwabcinsa, Henry Ekwos, zuwa ɗakinsa da nufin ya zo ya taimaka masa wajen saita masa manhajar ‘WhatsApp’ a wayarsa.

“Shi kuwa yaron bisa rashin sanin abin da aka shirya masa sai ya amince ya shiga ɗakin tare da shi bayan kuma ya rigaya ya haƙa rami.

“Ganin ramin da aka haƙa a ɗaki ya sanya yaron zargin wani abu lamarin da ya sa ya juya ya fita a guje inda shi kuma Chukwura ya bi bayansa ɗauke da adda tare da sassara shi a wurare da dama a sassan jikinsa.”

Abattam ya ce yaron bai daina gudu ba tare da ihun neman ceto, cikin sa’a sai wasu da suka fahimci halin da ake ciki suka taimaka wajen sanar da ‘yan sandan da ke sintiri a yankin a wannan lokaci kana daga bisani aka cafke Chukwura.

Jami’in ya ci gaba da cewa, ba a ɓata wani lokaci ba wajen garzayawa da yaron da lamarin ya shafa zuwa wani asibitin gwamnati da ke kusa don ba shi agajin gaggawa, yayin da aka tafi da Chukwura zuwa ofishin ‘yan sanda.

Ya ƙara da cewa wanda ake zargin bai faɗa musu wata ƙwaƙƙwarar hujjar da ta ingiza shi yin yunƙurin halaka ɗan makwabcin nasa ba, amma cewa ramin da ya haƙa a tsakar ɗakinsa ya yi haka ne kawai don ya baƙanta wa maigidan rai saboda umarnin ya bar masa gida da ya ba shi.

Sai dai matar mutumin, Ezinne Anyanwu, ta faɗa wa ‘yan sanda cewa maigidan bai ba su kowane umarnin su bar masa gida ba, abin da dai ta sani ana bin su kuɗin haya na wasu ‘yan watanni.

Ta ci gaba da cewa, a ranar 5 ga Janairu, ta ƙalubalanci maigidan nata game da ramin da ya haƙa a cikin ɗaki, sai ya ce mata wai yana neman dalolin da ya binne ne a ƙasa.