In Sha’Allah sai Allah Ya kunyata fasiƙan cikinmu kuma ya shirye su

Daga MUSTAFA KABIR SORON ƊINKI

Allahu Akbar! Gaskiya idan ni ne Malam Aminu Ibrahim Daurawa sai na sheƙa kuka saboda farin ciki. Tunda abun ya faru a game da shi a kan sha’anin na shiga cikin “Opinion poll”. Gaskiya Allah bai bar Shaiɗan ya yi galaba a kan mutanen Kano da soyayyar wani abu wanda ya fi addininsa ba.

Ban ji daɗin abun da ya faru tsakanin Malam da Gwamnan Kano ba. Amma kuma na yi farin ciki yadda na ga mutane cikakkun ‘yan kwankwasiyya suna bayyana damuwarsu ƙarara a kan haka. Idan na ce mutane, ba fa ina nufin ‘yan Kwankwasiyyar mazava ba. Manyan ‘yan Kwankwasiyya waɗanda wasu abokaina ne kuma na san ƙarfinsu a tsarin. Allah Ya qara mana son addininSa.

Gaskiya na yi farin ciki da aka sulhunta Malam ya ci gaba da yaƙi da fasiƙai a garin Kano. Ita kuma Murja. Abun da ya faru a wancan lokacin ai baƙin jini ya ƙara mata ba ɗaukaka ba. Idan ka duba sharhin mutane a kanta sai ka dinga tausaya mata. Akwai wanda na ji ya ce wai da ya haifi irinta gwara Allah ya hanashi haihuwa har ya mutu. Rashin haihuwa masifa ce amma shi ya fi masa alheri a kan ya samu irinta. Bala’i kenan.

Ban tava zaton gwamna zai bar irinta su zo kusa da shi ba ma. A sanin da na yi wa Kwankwaso daga nesa. Bai yarda da rashin manufa ba a rayuwa. Ballantana abin da zai sa ya rasa mutum mai amfani a siyasarsa. Malam Daurawa ya fi kwamishina goma amfani a Kwankwasiyya. Shi magoya bayansa babu wanda ya san adadinsu sai Allah. Ko shi Malam ɗin bai sani ba. Na tabbata, babu wanda zai zaɓi wani ɗan siyasa saboda Murja sai ɗan balaja’u irinta.

Mu na fatan wannan saɓanin zai zamo alheri ga hukumari Hisbah ɗin In Sha’Allah. Ita kuma mu na fatan za a gaggauta yi mata hukunci akan iskancin da ta ke yi mana a garinmu ko kuma ta bar mana jihar. Allah ya shiryar da mu bakiɗaya.

Mustafa Kabir Soron Ɗinki marubuci ne kuma mai sharhi a kan al’amurra na yau da kullum. Ya rubuto daga jihar Kano.