Ina ƙarami na yi wa mahaifiyata tallan kayan girki – Kamaye

Daga UMAR GARBA, a Katsina

Ɗan Azumi Baba wanda aka fi sani da Kamaye a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’ na tashar Arewa 24 baya ga kasancewar sa ɗaya daga cikin mutanen da suka ƙirƙiri masana’antar shirya finafinai ta arewacin Najeriya, wato Kannywood, ya kuma yi fice a fannoni daban daban na rayuwa kama daga rubuta littattafai, mashiryin shiri gami da bada umarni a finafinan da masana’antar ta kwashe shekaru tana shiryawa. Wakilin Manhaja a Katsina Umar Garba, ya haɗu da fitaccen jarumin a wurin taron ƙungiyar marubuta ta arewacin Najeriya da ya gudana a jihar inda ya tattauna da Kamaye kamar yadda aka fi sanin shi a kan batutuwan da suka shafi taƙaitaccen tarihinshi, kasancewar shi marubuci, jarumi, mai shirya fim gami da bada umarni, nasarori da kuma ƙalubalen da ya fuskanta a rayuwarsa.

BLUEPRINT MANHAJA: Za mu so jin taƙaitaccen tarihinka?

KAMAYE: Sunana Ɗan Azumi Baba Ceɗiyar ‘yan Gurasa, tsohon marubucin littattafai wanda yanzu ake kira Kamaye ko Awon igiya a tashar Arewa 24 cikin shirin ‘Daɗin Kowa’ wasa farin girki.

An haife ni a Ceɗiyar ‘yan Gurasa cikin birnin Kano a ƙaramar Hukumar Dala, haka nan kuma na ɗan tava abubuwa wanda a rayuwa akewa matashi. Na yi karatun makarantar allo a wurin malam Ma’azu Aliyu Makwarari na kuma yi karatun ilimi a wajen Malam Musa Ceɗiyar ‘yan Gurasa, daga nan na koma wurin abokina wanda ya zama malami na wati Malam Iro yan muruci.

Me ya sa kafi fitowa a matsayin talaka a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’ dama wasu finafinai da ka fito?

Maƙasudin fitowa ta a role ɗin talauci ba don kome ba sai don in nuna wa talakawa cewa, yayin da ka tsinci kanka cikin masifar talauci da rashi abinda zaka fara ɗaukowa ka riƙe shine addu’a da bin Allah, kuma ka zama mai haƙuri idan matarka ta taso maka sai ka bata haƙuri daga nan sai kai waje kamar yadda mu kai ta faɗi tashi da Adama har tura ta kai bango na haƙura duk da talauci na daga ƙarshe Allah yai min kyautar Kyauta Dillaliya wadda nike ce wa ‘yar aljanna (dariya).

Baya ga wannan jama’a su kan ce rawar da tafi dacewa dani in taka a fim ita ce talauci kasan ba kowa ke son fitowa a talauci ba, kowa ya fi son ya saka babbar riga da sauran su.

Kawo yanzu za ka iya faɗa wa masu karatu finafinai nawa ka fito a matsayin jarumi?

Gaskiya finafinan su na da yawa kamar yadda na faɗa ma ku baya ga fitowa a matsayin jarumi Ina bada umarni, Ina rubuta labarai kuma Ina shirya finafinai saboda haka fitowa ta a cikin fim jefi-jefi ne, duba da cewa, Ina taka rawa daban daban tun farkon kafuwar masana’antar.

Sunanka ya yi fice amma a ‘yan shekarun baya masu kallon finafinai sun daina ganin ka a akwatin talabijin ɗin su kafin daga baya ka zama jarumi a shirin ‘Daɗin Kowa’ na tashar Arewa 24. Ko me ye dalilin daina ganin ka da aka yi a baya?

Kamar yadda na gaya ma ku ni marubuci ne na zama marubucin finafinai, na zama mashiryin shiri na kuma zama darakta Ina kuma fitowa finafinai, amma tsalli tsalli ni ke fitowa ba gabaɗaya ba, don haka ban tashi samun kaina jarumi da ke fitowa a fim ba sai cikin ‘Daɗin Kowa’ wannan ya faru sakamakon wasu yara da suka taso ƙarƙashina wanda Allah ya ba su dama shine suka ga tunda dama ta samu bari su taimake ni daga cikin su akwai Mustapha (Mista Indiya), Musa A.Musa (Balarabe Turufa),T. Balarabe, Zuwaira marubiya, Fauziyya D. Suleiman, Ɗan rimi da kuma Yakubu Liman.

Waɗannan mutanen su ne su ka taimaka min wajen fitowa ga bakiɗaya ba kamar yadda ni ke fitowa a da ba, wato jefi-jefi.

Kafin ka shiga harkar fim wacce sana’a ce ka yi a baya?

Ɓangaren sana’o’i na yi sana’a iri daban-daban tun Ina ƙarami na yi wa mahaifiyata tallan kayan girki misali, tattasai, albasa, tumatir, haka zalika mahaifina ɗan koli ne na ma shi tallan soso da sabulu irin na da a kasuwar Sabon Gari tun tana bunu, daga nan na koma wurin yayana Muhammadu wanda mu ka yi kasuwanci tare a Sabuwar Kasuwa ta Ƙofar Wambai, daga nan kuma a cikin birnin Kano wanda daga nan kuma na koma hannun yayana Aliyu wanda muka zauna a kantin kwari daga kantin kwarin ne Allah yai juyinsa na shiga makarantar yaƙi da jahilci ta shahuci ta Barden Madawaki Baban Ladi Sakatima Allah ya jiƙan shi, anan na taɓa karatun zamani Allah yai wa abin albarka na zama marubuci, daga harkar rubutu ne da muka ga matasa sun ɗan yawaita sai muka tsallaka muka ƙirƙiri masana’antar fim wato wadda ake kira Kannywood a yanzu, daga harkar littafi muka samar da wannan masana’anta wadda ta ke da ɗimbin jama’a wanda yanzu ga shi matasa da dama sun sami aikin yi.

Kasancewar masana’antar Kannywood ta samo asali ne bayan da ka yi tunanin sauya akalarka daga rubutu zuwa harkar shirya fim. Shin mu na iya cewa a halin yanzu ka daina rubutun littattafai kenan?

A’a ban aje rubuta ba har gobe Ina yin rubuta in ajiye kuma a yanzu zancen da ake akwai littattafai guda bakwai suna nan tafe akan hanya wanda ni ke son su fito da sabon salo wato sabon salo na kasuwanci.

Za ka iya faɗa mana yawan littattafan da ka rubuta?

Gaskiya idan na ce zan faɗa ma ka to zanyi kuskure domin na sha rubuta littattafai in saka sunan wasu wato idan na ga mutum yana da son yai rubutu amma kuma Allah bai ba shi baiwar rubutun ba na kan rubuta labari in saka sunan shi.

Tun farko ka faɗa mana finafinan ka da kafi so. Shin ko za ka iya faɗa wa masu karatu a cikin littattafan da ka rubuta wanne ka fi so?

Akwai littafina ‘Rikicin Duniya’ Ina alfahari da shi, amma a yanzu cikin waɗanda za su fito akwai zakaran gwajin dafi wanda shine cikamakin littattafan da na fi so wanda shine ‘Ilimi Kwanso’.

Zamu so mu ji batun iyali fa?

Ina da matana uku, sai yara na sha huɗu 14, masu rai banda waɗanda suka rasu.

Me ya kawo ka Jihar Katsina?

Taron marubuta wanda aka saba yi duk shekara kuma duk lokacin da za a yi su Bilkisu Yusuf Ali da Dakta Bashir Abu Sabe da kuma Ɗan juma Katsina su kan kira ni duba da cewa dukkan su abokan arziƙi ne kuma ana tare duk abinda za su yi su kan kira ni kuma na kan zo na halarci taron idan wani abin bai gitta min ba.

Ɗan Azumi Baba

Ko za ka gaya mana ƙalubale da kuma nasarorin da ka samu a rayuwa?

An fuskanci ƙalubale kam saboda duk wanda ya samu nasara sai da ya fuskanci ƙalubale sai dai bai kamata ƙalubale ya hanaka cimma burinka na rayuwa ba. Alhamdulillah an samu nasarori waɗanda idan za mu yini bazan iya lissafa ma ka su ba, saboda har yanzu ana kan samu sai dai mu cigaba da gode wa Allah.

Daga ƙarshe wane saƙo gare ka ga masoyanka?

Masoyana na duniya bakiɗaya maza da mata, manya da yara, Ina godiya Allah ya saka da alheri, Allah kuma ya bar zumunci.

Mun gode da lokacinka da ka ba mu, muka tattauna da kai.

Kuma masu ɗaukar wannan tattaunawa na gode maku.