Daga MAHDI M. MUH’D
Khadija Ahmed Lame, uwargidan fitaccen marubuci a dandalin sada zumunta, Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata, ta bayyana fatanta na cewa maigidanta zai dawo gida wata rana.
Ranar Laraba, 2 ga watan Agusta ake cika shekara huɗu da ɓatan Abubakar Idris, shahararre kuma marubuci a shafukan sada zumunta.
A watan Agustan 2019 ne aka bi shi har gida a daidai lokacin da ya dawo daga tafiya, inda aka sace shi da motarsa.
Tun sace shi da aka yi daga gidansa ba a sake jin labarinsa ba. Tun daga lokacin wasu suka zargi hukumar tsaron farin kaya ta DSS da ɗauke shi, sai dai hukumar ta musanta zargin. A baya an sha samun kiraye-kirayen sakin sa daga ‘yan uwa da abokan gwagwarmayar matashin.
“A irin wannan rana ce wasu mutane ɗauke da makamai suka yi garkuwa da Abubakar Idris (Dadiyata), wanda ya shahara wajen sukar gwamnatin Nijeriya a shafukan sada zumunta, a gidansa da ke Kaduna,” a cewar Ƙungiyar Kare Haqqin Bil’adama ta Amnesty International cikin wani saƙo a shafinta na Tiwita.
Kafin sace shi, Abubakar Dadiyata ya yi fice wajen sukar manufofin gwamnatinjihar Kano ta lokacin da kuma ta tarayya.
Matarsa Khadija Abubakar Dadiyata ta bayyana wa manema labarai cewa, halin da ta tsinci kanta tun bayan sace mijin nata.
‘’Mun tsinci kanmu cikin halin baƙin ciki da damuwa sakamakon rashin sanin inda yake, mun shiga mun fita wajen shugabanni duk inda za mu je mu kai kukanmu, mun je mun kai kukanmu’’.
Ta ce, ba ta ɗauka za a kawo wannan lokaci mai tsawo haka ba tare da sakin mijin nata ba.
“Ban ɗauka abin zai kai kwanaki masu yawa ba, amma yanzu ga shi har shekaru huɗu,’’ inji ta.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya yi alƙawarin gudanar da bincike kan ɓacewar Didiyata.
Sai dai matarsa Lame ta ce, har yanzu ba a tuntuɓi dangin ba kan wani bincike da aka gudanar.
“Da farko an so mu yarda cewa ana gudanar da bincike, amma har yanzu babu wani abu da ya fito daga ciki.
“Babu wanda ma yake magana da mu, sai dai alƙawarin da gwamnan Kano ya ɗauka kwanan nan. Kuma ban ma sani ba ko sun fara binciken kamar yadda suka yi alƙawari saboda babu wanda ya tuntuɓe mu,” inji ta.
Lame ta kuma bayyana cewa tana yi wa ‘ya’yanta biyu ƙarya cewa mahaifinsu ya yi tafiya kuma zai dawo nan ba da daɗewa ba.
“Yaran sun fara surewa da ni, domin na sha yi musu ƙarya cewa mahaifinsu ya yi tafiya kuma zai dawo nan ba da daɗewa ba. Tambayoyi su ke min akodayaushe, kuma ina ba su haƙuri da cewa zai dawo nan ba da daɗewa ba,” inji ta.
Dangane da yadda dangin suka kasance cikin shekarun da suka gabata, ta ce abokai da dangin mijinta da ya ɓace suna tallafa wa mata.
Da aka tambaye ta ko har yanzu tana da begen sake saduwa da mijinta, mahaifiyar ’ya’yan biyu ta ce, “Na yi imani zai dawo. Ban tava tunanin cewa ya tafi har abada ba. Za mu sake haɗuwa, da yardar Allah. Don haka ina da kwarin gwiwa cewa zai dawo.
“Ina kira ga sabuwar gwamnati da duk wanda ke da ikon ceto mijina da ya yi haka, don Allah. Ina tsoron kada duk ƙaryar da nake yi wa ’ya’yana ta ƙare.
“Kowace rana mai albarka, ina roƙonsu da kada su damu mahaifinsu zai dawo. Kuma har yanzu bai dawo ba. Ba na son yaran su gan ni a matsayin maƙaryaciya.”