Ina da burin taimaka wa ƙananan mawaƙa da marubuta – Aliyu Al’usku 

(Ci gaba daga makon jiya)

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

MANHAJA: Waɗanne nasarori ko ƙalubale aka fuskanta kawo yanzu, a cikin harkokinka na waƙa? 

AL’USKU: Na samu nasarori masu yawa da ba zan iya lissafa su ba, na samu karramawa da kyautuka masu yawa daga masoya da na sani da waɗanda ban sansu ba ma. Alhamdulillah. 

Batun ƙalubale fa? 

To, Alhamdu Lillah, babu wani abu na alkhairi da babu ƙalubale a cikinsa. Game waɗannan ayyukan rubutawa da rera waƙoƙi da nake yi, na fuskance su iri daban daban. Ba alfahari ba, kamar yadda duk masu bibiyar waƙoƙina suka sani, na fi mayar da hankali a kan waƙoƙin faɗakarwa da kuma wa’azantar da al’umma a kan wasu matsalolin zamantakewa, gurɓacewar tarbiyya. Kamar shaye-shaye, fyaɗe, ta’addanci da kuma kira don a zauna lafiya da ciyar da al’umma gaba, musamman ‘yan’uwana matasa da su ne ƙashin bayan kowacce al’umma.

Haka zan zuba kuɗina bayan lokacina, na yi ayyuka na sa a gidajen rediyo da kafafen sadarwa. Amma a hakan ma sai ku ga sai mun dinga bayar da wani abu na goro sannan ake sakawa don saƙon ya isa ga waɗanda aka yi domin su.

Idan muka ɗauki lokaci ba ku bayar da ɗan na goron ba, sai mu daina jin ana sakawa. Kuma fa hakan na faruwa ne don kawai mu ba wasu ba ne da duniya ta sanmu. Amma kuma abin mamaki, wasu nasu ayyukan ba su ko kusa da namu ba ta fuskar amfanar da al’umma, sai ka ji ana ta sakawa alhali kuma ba su san ma ana yi ba. Ba wai hassada ba ce, amma dai akwai ciwo a nuna maka ƙyashi ko rashin tanyo ga wanda ba kowa ba ne shi, amma da zaran ya zama wanin (ɗaukaka) sai ka ga ana ta nan-nan da shi.

Ta fuskar sauran al’ummar gari kuma, su da kansu sun san ayyukan alkhairi mutum yake yi, kuma wasu za su iya bashi gudunmawa da zai samu ƙarfin gwiwa ya faɗaɗa ayyukan, amma kuma ba za su yi hakan ba, sai dai ma ka ga suna ƙoƙarin yin daɓe a kufai!

To, ta yaya masu kyakkyawan tunani da son kawo nagartaccen canji cikin al’umma za su samu ƙarfin gwiwa idan ana tafiya a haka?

Hukumomin gwamnati da ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba ma na da nasu laifi, maimakon su tallafawa ire-iren waɗannan mutane, sai ka ga ana ƙarawa masu ƙarfi taki, bayan kuma su dama sun riga sun ginu ko babu wani abu mai kama da wannan za su iya tafiyar da harkokinsu.

Waɗanne waƙoƙi ka yi waɗanda za ka iya cewa sun cancanci yabo, saboda saƙonnin da ke cikinsu? 

Kamar yadda na gaya maka a baya na yi waƙoƙi da dama, amma irin waɗanda ka ke magana akai na faɗakarwa sun haɗa da waƙar ‘Alaƙar Tarbiyya da Tsaro’, waƙar ‘Rashin Tarbiyya da Hanyoyin Shawo kan Matsalar’, ‘Kira Don a Yi Katin Zaɓe da Fita Zaɓe’, ‘Jan Hankali Akan Wanda Ya Cancanta A Zaɓa’, (Nagartacce). Akwai waƙar ‘Illolin Bangar Siyasa’, ‘Illolin Fyaɗe da Hanyoyin Magance Matsalar’, ‘Kira Ga Matasa Don Gujewa Kayan Maye’, ‘Zaman Lafiya da Juna’, sai kuma waƙar ‘A Yi Zaɓe Lafiya Kar A Yi Tashin Hankali’. 

Waɗannan da wasu ma da ban ambata ba, duk na yi su ne don wayar da kan jama’a da ilimantarwa, amma duk da hakan babu wani mutum a hukumance ko ƙungiya da suka yi ko da jinjina bare ɗaukar nauyin tallata ayyukan don su kai lungu da saƙo don amfanar da al’umma. Na tabbata da a ce waƙoƙin da na yin sun zama akasin hakan, ko na ci zarafin wani, da yanzu ina ɗaure ko kuma na shiga gidajen gyaran hali ya fi sau shurin masaƙi. 

To, amma Alhamdulillahi, ba mu gaji ba, ba kuma za mu gaji ɗin ba. In sha Allahu Ta’ala, za mu kai har mu wuce inda duk ake tsammanin zuwanmu.

Wanne gyara ko sauyi ka ke ganin za ka iya kawowa, idan ka samu goyon bayan da ka ke buƙata?

Ko kawo yanzu ma na yi abubuwa da yawa, duk da babu ɗaukar nauyi ko tallafin wani. Amma idan da zan samu tallafi daga gwamnati ko ƙungiyoyin cigaban al’umma, akwai ayyuka da dama da za mu yi don faɗakarwa ga halayyar zamantakewar al’umma, ko wasu tsare-tsare da manufofin gwamnati. 

Sannan a nawa ɓangaren, ina da burin ganin na taimakawa wasu ƙananan mawaƙa da marubuta, waɗanda Allah Ya ba su zallar baiwa da fasaha, amma kuma rashin damar wallafawa take kawo musu naƙasu. Allah ne shaida, ni na san irin wahala da na sha ko in ce nake a wannan ɓangaren, duk da yake a yanzu kam Alhamdulillahi an fara samun damar da ake nema ɗin.

Amma dai ni na san zunzurutun matasa fasihai daga maza da mata, amma rashin masu kama hannayensu da jansu a jiki ko ba su gudunmawar wallafa ayyukansu ke sa kullum suke komawa baya a maimakon su cigaba. Wasu ma daga nan ne suke samun sagewar gwiwa sai su watsar da ayyukansu na adabi.

Wannan mummunar asara ce garemu, ba iyakar su kaɗai ba har ni da kai da ‘ya’yanmu masu tasowa nan gaba, saboda Allah ne kaɗai Ya san mai taimakon wani a rayuwar nan. Ina roƙon Allah Ya bani damar da zan amfanar tare da samar da canje-canje na alkairi a cikin wannan harka tamu ta Adabi. Amin.

Yaya alaƙarka take da sauran marubuta waƙoƙi da adabi? Ko su wane ne abokan hulɗarka na kusa a cikinsu?

AlhamduLillah, babu shakka ina da kyakkyawar fahimta da alaƙa da kowa.

Ba na raina kowa kuma babu mai raina ni. Ni na kowa ne, kuma kowa nawa ne. 

Bayan harkar waƙe-waƙe da rubuce-rubuce wanne aiki ko sana’a kake yi?

Sosai kuwa! Malam Bahaushe yana cewa, ‘Da ruwan ciki ake jan na rijiya.’ Kamar yadda na faɗa a baya, tun farkon zuwana Kano a ƙarshen shekarar 2009 bayan kammala makarantar sakandire, na fara sana’o’i a nan Kano.

Alhamdulillah, mafi girma da shahara a sana’ata ita ce harkar magungunan gargajiya da na Musulunci, wato aikin ba da maganin Herbal and Islamic Medicine. Ina kuma yin sana’ar sayar da kayan soye-soye, irin su cincin, da fanke, ina rabawa a shagunan sayar da lemon kwalba, a farashin sari. Sannan kuma ina saye da sayarwa na wayoyin hannu har ma da na’urori masu ƙwaƙwalwa (Computers) sababbi da kuma waɗanda aka yi amfani da su. A haka dai muke ta gwagwarmaya Allah Yake rufa mana asirin yau da kullum.

Shin za ka so wani a cikin zuriyarka ya gaje ka a fannin rera waƙoƙi?

Ko shakka babu zan so yarana su gaje ni a fagen waƙoƙin da nake yi. Ko da kuwa masu gadon sun kasance mata ne. Matuƙar dai za su iya kiyaye haƙƙoƙin Allah da Manzonsa tare da kare mutuncinsu da na iyaye da zuri’arsu kamar yadda nake ƙoƙarin yi. Idan dai sun kaucewa duk wani abu da zai zubar musu da mutunci kuma sun yi domin Allah, to sakamakonsa zai riske su tun a nan gidan duniya da kuma lahira kamar yadda muke fatan samun namu sakamakon in sha Allahu Ta’ala. 

Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarka?

Akwai karin magana da dama da suke tasiri a rayuwata, irinsu: Alheri danƙo ne, Zama lafiya ya fi zama ɗan sarki, Sannu ba ta hana zuwa, Wani hanin ga Allah baiwa ne, faɗi alkairi ko ka yi shiru! Guntun gatarinka ya fi sari ka bani, Hassada ga mai rabo taki ce! 

Na gode ƙwarai da gaske.

Ni ne da godiya. Ina kuma so in yi amfani da wannan da dama don isar da saƙon gaisuwata, godiya da jinjina ga duk ma’abota saurare da karanta waƙoƙina.