Daga MUKHTAR YAKUBU
A ‘yan kwanakin da suka gabata ne aka yi wani taro na tantance jaruman da za su fito a wani sabon fim da Kamfanin Mai’atamfa Warure Mutimidia yake shirin fara aikin sa nan da ɗan lokaci mai zuwa.
Taron tantancewa da aka gudanar a ofishin kamfanin Mai’atamfa Warure Mutimidia da ke Ƙofar Dukawuya a kan titin zuwa Tsohuwar Jami’ar Bayero a cikin garin Kano, ya ɗauki wani sabon salon da ba a saba ganin irin sa ba a duk lokacin da aka shirya taron tantancewa Jaruman da ake son shigar su cikin wani fim. Domin kuwa aƙalla jaruman da suka halarci wajen mazan su da matan su, sun kai kusan 500 wanda kuma a cikin su akwai tsofaffin jini da aka san fuskar su , da kuma jarumai masu tasowa.
Kabiru Lawan Mai’atamfa Warure, shi ne Babban Furodusa na wannan sabon fim ɗin kuma shi ya shirya taron tantance jaruman. Don haka ne bayan an kammala taron, wakilinmu ya tattauna da shi dangane da shirin da ya yi na samar da fim ɗin da kuma manufar sa ta shiryawar. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance.
MANHAJA: Da farko za mu so ka gabatar da kanta ga masu karatun mu.
Kabiru Lawan Mai’atamfa Warure. To ni dai sunana Kabiru Lawan Mai’atamfa Warure kuma ni ne Shugaban Kamfanin Mai’atamfa Warure Mutimidia wanda yake shirya finafinai a masana’amtar finafinai ta Kannywood wanda a yanzu ma abin da ya tara mu a wannan waje kenan, domin tantance jaruman da za mu yi amfani da su a cikin sabon fim ɗin da za mu shiga aikin sa a nan gaba kaɗan.
Kuma tantance jaruman da muka yi a bisa shi wannan fim ɗin da za mu shiga. Ana son a samar da wasu mutane ne da adadin su ya dace da shekaru da kuma yanayin jaruman da aka samar a cikin fim ɗin wanda mun kasa abubuwan zuwa kaso shida zuwa bakwai . Kuma cikin ikon Allah an zo an tantance. Kuma Alhamdulillah waɗanda suka zo aƙalla sun kai 584, wanda a yanzu wasu sun yi nasara, wasu kuma suna daf da yin nasarar. Kuma ko da mutum bai samu ba a yanzu, to zuwa nan gaba zai iya samu a tafi da shi.
To shi wannan aikin da za ka yi shi, ko shi ne na farko a gare ka?
Ai na yi furodusin ɗin finafinai a baya kamar fim ɗin ‘Bimbini’ da na yi a wajen ɗan’azumi Baba. Sai kuma a wajen Hamisu Ayagi, shi ma na yi fim ‘Makarantar Bosho’, sai kuma fim ɗin Rahama Amma sun daɗe fa, ba na yanzu ba ne, don na shiga harkar tsawon lokaci daga baya na bar ta saboda wasu dalilai da suka sa na ji ba na buƙatar ta, sai kuma a yanzu da na dawo na buɗe ofishina na taho da ƙarfina, kuma da izinin Allah nake son na yi wannan fim ɗin.
To tsawon lokaci da ka shafe ba ka cikin harkar a yanzu da ka dawo ya ya ka same ta?
A gaskiya harkar na same ta a yanzu ta canza ta kowanne ɓangaen fiye da yadda na san ta a baya, don haka abubuwan da ake gudanarwa a yanzu saboda da ci gaban zamani sun sa an samu sababbin tsarin da babu su a baya .
Kamar yadda ka faɗa abubuwan sun canza. Daga cikin abubuwan da suka canza har da harkar kasuwancin fim cin.
A matsayin ka na wanda za ka zuba kuɗi ka yi harkar a yanzu wanne irin shirin ka yi?
E a baya idan muka yi fim sai mu buga shi ne a a CD mu kai kasuwa mu sayar . To amma a yanzu harkar ta canza sai dai a saka fim ɗin a You tube ko kuma wani daga cikin manyan gidajen talabijin ku daidaita da su. To mu Alhamdulillah tsarin da muke da shi muna da tsarin mu kai shi Niɗfils ne da sauran manyan gidajen talabijin. Wannan ne ma ya sa muka ware kuɗaɗe masu yawa da za mu kashe domin samar da fim ɗin da zai zama na daban a cikin finafinai da aka saba yin su a cikin wannan masana’amtar ta Kannywood. Kuma da yardar Allah za mu kai ga yin nasarar da muke buƙatar samu.
Kamar zuwa wanne lokaci ake sa ran za a fara aikin fim ɗin?
To da yake daman mun shirya wa aikin, da yardar Allah nan gaba kaɗan a bayan Sallar nan za mu shiga aikin. Kuma a gaskiya ma ba fim ɗaya za mu yi ba, don mun ware za mu yi finafinai guda uku ne a lokaci guda duk a jere za mu yi su
Kowanne fim akwai manufarsa da kuma saƙon da yake son ya isar. Shi wannan fim ɗin wanne saƙon ake so ya isar ?
E shi fim ɗin sunan sa ‘Mutum da Amana’, kuma yana son ya isar da saƙo ne a game da keɓancewa a tsakanin namiji da mace , duk da yake shi ne jigon labarin, amma akwai saƙonni da dama da suka zama rassa a cikin fim ɗin wanda ba sai mun buɗa shi dukka a jarida kowa ya sani ba, saboda abu ne da sai fim ɗin ya fito mai kallo zai ga abin da ya ƙunsa .
Wanne irin fata kake da shi a game da wannan aikin naka?
To har kullum ina fatan yin nasara ne. Kuma ka san ita nasara daga Allah take a kullum fatan mu kenan, saboda haka ba na fitar da rai da yin nasara a cikin wannan aikin, don haka muna sa ran mu yi nasara ɗari bisa ɗari a cikin aikin.
Ko menene saƙon ka na ƙarshe?
To abubuwan da za su zamo saƙona na ƙarshe shi ne kira da zan yi ga su shugabannin masana’amtar finafinai ta Kannywood ya kamata mu farka, saboda abokan sanar mu na Kudu, sun yi mana nisa sosai saboda taimakon na ƙasa da su da suke yi da kuma haɗin kai da suke da shi, kuma ba su da handama da babakere. Don haka Ina kira da a haɗa kai tare da taimakon juna sannan mu rabu da nuna ɓangaranci kamar yadda ake yi a yanzu idan abu ya samu wani sai a rinƙa kallon shi ɗan ɓangaren wane ne. To don Allah mu haɗa kai mu samu damar da za mu inganta sana’armu.