Ina da yaƙini NNPP za ta samu gagarumar nasara a zaɓukan 2023– Kwankwaso

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso ya ce Jam’iyyar NNPP za ta samu gagarumar nasara a zaɓukan 2023.

Kwankwaso ya bada wannan tabbaci ne a yayin taron Kwamitin Ƙoli na jam’iyar da ya gudana a jiya Asabar a Abuja.

Kwankwaso ya ce ƴan Nijeriya na ta tururuwa wajen shiga jam’iyar mai alamar kayan marmari.

Ya kuma yi kira ga sauran jama’a da su gaggauta yin rijista da jam’iyar domin su shiga zaɓukan da za a yi a ƙarƙashin jam’iyar.

“Ina mai tunatar da mutane cewa an ci gaba da sayar da fom ɗin shiga takarar majalisun dokoki na jiha da ma sauran gurabe ga waɗanda ke da sha’awar tsayawa takara.

“Ina son na ja hankalin kowa ya zama yana da hangen nesa. Wannan jam’iyar ta mu ta duk ƴan ƙasa ce da su ka yarda da ci gaban ƙasar nan.

“Ina kira ga kowa da ya je mazaɓar sa ya yi rijista. Fom ɗin mu bashi da tsada. Na shugaban ƙasa ma ba Naira miliyan 100 ba ne,” a cewar Kwankwaso

A nashi ɓangaren, Shugaban NNPP na ƙasa, Farfesa Rufai Alkali ya ce an kafa jam’iyar ne da manufar tabbatar da dimokaraɗiyya da kuma ceto Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *