Ina dalilin da ya sa Beijing ta zama zakaran gwajin dafi wajen shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu?

Daga CRI HAUSA

A wajen bikin rufe gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta bana, wanda aka yi jiya Lahadi a birnin Beijing, fadar mulkin ƙasar Sin, shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics ta ƙasa da ƙasa wato IOC, Mista Thomas Bach ya gabatar da jawabi, inda a cewarsa, gasar Olympics ta bana, gasa ce da ba’a taɓa ganin irinta ba a tarihi.

Kwamitin IOC shi ma ya yi irin wannan tsokaci game da gasar wasannin Olympics ta lokacin zafi, wadda aka gudanar a Beijing shekaru 14 da suka wuce. Tun daga shekara ta 2008 zuwa bana, ƙasar Sin ta shaida wa duk duniya cewa, ita ƙasa ce dake tsayawa haiƙan kan manufar gasar Olympics, tare da aiwatar da ita yadda ya kamata.

Abu mafi muhimmanci a nan shi ne, ganin yadda cutar COVID-19 da sauran wasu ƙalubaloli ke ci gaba da addabar al’ummomin duniya, Beijing ta yi nasarar gudanar da gasar Olympics cikin lokaci, al’amarin da ya ƙara inganta haɗin-gwiwa da zaman lafiya a duk faɗin duniya. Bach ya kuma ce, haɗin-gwiwa a wajen gasar Olympics, ta fi ‘yan a-ware ƙarfi. Har ma shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics ta ƙasar Ukraine Sergey Nazarovich Bubka ya ce, sakon da gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu da aka yi a Beijing ta aikewa duniya shi ne, ‘yan Adam za su iya zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya, wajen samun galaba kan cutar COVID-19.

Fassarawa: Murtala Zhang