Ina duba yiwuwar ƙarin albashin ma’aikata – Tinubu

Daga WAKILINMU

Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Nijeriya ya bayyana cewa nazarin yiwuwar yi wa ma’aikata ƙarin albashi.

Ya bayana haka ne a jawabin da ya yi wa ‘yan ƙasa da yammacin ranar Litinin.

Ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta ɗauki tsauraran matakai ne saboda sun zama dole, “kuma babu waɗanda suka fi su sauƙi.”

Ya ce, “Da a ce akwai hanyoyin da suka fi su sauƙi da na bi.

“Abin da zan iya yi kawai shi ne ɗaukar matakan da za su sauƙaƙa yanayin.

“Gwamnatina za ta tabbatar da yin aiki tare da dukkan jihohi don rage raɗaɗin da ’yan ƙasa ke ji,” in ji shi.