Ina fatan sake zama tsohon Shugaban Ƙasa – Buhari

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ce, ya na fata ya sake zama tsohon Shugaban Ƙasar Nijeriya, saboda ba shi da niyyar zarcewa a karo na uku.

A ranar Alhamis a garin Lafiya, Babban Birnin Jihar Nasarawa, ne ya bayyana cewa, shugabannin da suka yi rantsuwar mulki da littafi mai tsarki dole ne su yi taka-tsantsan, don kada su ci amanar shugabancin jama’a da Allah ya ɗora masu.

Da ya ke jawabi a wata ziyarar ban-girma da ya kai fadar Mai Martaba Sarkin Lafiya, Alhaji Sidi Bage Muhammad I, shugaban ƙasar ya ƙara tabbatar da cewa, ba shi da niyyar sake tsayawa takara bayan wa’adin mulki na biyu da tsarin mulki ya amince da shi a matsayin Shugaban Nijeriya.

“Muƙamin sarkunan gargajiya gado ne. A tsarin mulkin qasa, mu (zaɓaɓɓun masu riƙe da muƙaman gwamnati) ba haka ba ne. Ba zan iya wuce wa’adi na biyu ba kuma na rantse da Alƙur’ani mai girma cewa zan kiyaye kundin tsarin mulkin Tarayyar Nijeriya,” inji Buhari.

Ya ƙara da cewa, “bayan siyasa, a duk lokacin da aka samu yin rantsuwa da Alƙur’ani mai girma, dole ne mu yi taka-tsantsan. Mu tabbatar da cewa, ba mu ci amanar da Allah ya ba mu a matsayin shugabanni ba. Na ga tsofaffin gwamnoni a nan, kuma Ina fatan ni ma na zama tsohon Shugaban Ƙasa.”

Shugaban ya gode wa al’ummar Jihar Nasarawa da suka yi masa kyakykyawan tarba, inda ya nuna jin daɗinsa da yadda jihar ta Arewa ta tsakiya ta sanya sabon salo tun bayan ziyararsa ta ƙarshe a shekarar 2019.

Ya kuma taya tsohon Gwamna kuma Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Kudu Sanata Umaru Tanko Al-Makura da mai ci Gwamna Abdullahi Sule murna bisa kyawawan ayyuka da nasarorin da jihar ta samu.

Da yake tarbar shugaban ƙasa a fadar da ta cika shekaru sama da 200, Sarkin Lafiya ya gode masa bisa kawo ƙarshen matsalar rashin isasshiyar wutar lantarki a jihar Nasarawa tare da samar da tashar wutar lantarki mai ƙarfin 330kVA.

Sarkin wanda shi ne Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Nasarawa, ya shaida wa Shugaban ƙasa cewa samar da wutar lantarki ya kawar da kashi 80 cikin 100 ne matsalar jihar.
Shugaba Buhari ya je Jihar Nasarawa ne, don ƙaddamar da wasu ayyukan raya ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *