Ina goyon bayan sauye-sauyen da Gwamna Raɗɗa ke yi a Jihar Katsina – Masari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana ra’ayinsa akan salon kamun ludayin Gwamnan jihar, Malam Dikko Umar Raɗɗa.

Masari ya bayyana ra’ayin na sa ne da yake jawabi a wurin wani taron liyafar cin abincin dare da Dattawan Jam’iyyar APC na jihar Katsina suka shirya domin karrama shi tare da yin addu’o’in samun nasara ga sabon Gwamnan da ta gudana a ɗakin taro na Paramount dake cikin birnin Katsina.

A cewar Gwamna Masari, yana tare da Dikko Raɗɗa ɗari bisa ɗari kuma yana goyon bayan sauye-sauyen da yake yi domin inganta harkokin mulkin jihar.

Masari, wanda ya ce ba zai yi katsalandan a harkokin mulkin magajin nasa ba, ya ƙara da cewa ya zama wajibi duk wanda yake tare da shi ya goyi bayan Dikko Raɗɗa domin yana da yaƙinin cewa zai kawo ma jihar ci gaba.

Shi ma da yake maida jawabi, Gwamna Raɗɗa ya sha alwashin cewa ba zai ba Gwamna Masari kunya ba ta hanyar cin amanar al’ummar jihar Katsina.

Daga ƙarshe kuma sai ya roƙi al’ummar jihar da su cigaba da yin haƙuri da shi musamman ma yanzu da yake aiwatar da wasu sauye-sauye domin cigaban jihar baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *