Ina son kafa gidauniya, sai dai ba na son a yayata manufuta – Zainab Santali

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Jigawa

Zainab Baba Aliyu Santali fitacciyar malamar makaranta ce a yankin masarautar Kazaure, kuma ita ce mace ta farko a Jihar Jigawa da take aikin jami’ar hulɗa da jamaa a jihar. Ta kasance ɗaya daga cikin mata matasa masu kishin addini. Wakilin MANHAJA a Jihar Jigawa ya zanta da ita a ofishin ta don jin wasu batutuwa da suka shafi rayuwar ta da kuma faɗi-tashin da ta sha. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Ma su Karatu za su so ki gabatar musu da kanki a taƙaice?
Assalamu alaikum. To Alhamdulillahi ni dai sunan Zainab Baba Aliyu Santali, an haifeni a garin Kazaure da ke Jihar Jigawa, a ranar 24 ga watan Maris,1998. Na yi karatuna na firamare a Kazaure, na yi sakandire na a FGC Kazaure. Da na gama kuma na fara aikin koyarwa a wata firamare da ke cikin Kazaure a matsayin malama.

Daga baya na koma karatu a BUK inda na yi karatun aikin jarida a shekarar 2006 zuwa 2009. Da na kammala karatun shi ne aka min sauyin wurin aiki na koma Ministry of Imformation. Su kuma suka tura ni ma’aikatar mata a matsayin PRO. Bayan haka ina da difuloma a ɓangaren ilimi, wato Post Graduate Diploma in Education. Haka zalika, ni mamba ce ta Nigerian Institute of Public Relations, kuma har wa yau ina riƙe da muƙamin sakatariya a Nigerian Association of Women Journalist ta reshen Jihar Jigawa.
Na zauna a ma’aikatar mata, na zauna a ‘Commerce’ yanzu ina ma’aikatar shari’a da ‘Economic Directory’, kuma ni ce PRO ta ‘Justice Sector and Law Reform Commission.

Akwai wasu abubuwa ne da ki ka sa gaba a halin yanzun don ganin kin kai ga cin musu, musamman na kasuwanci ko karatu ko kuma gwagwarmaya?
Eh gaskiya akwai su, domin na yi gwagwarmaya ko in ce ina kan yin ta musamman ta fuskar neman ilimin addininin musulunci, a ɓangaren karatun zamani da na addinin gabaɗaya mahaifi na ya yi min duk wata gwagwarmaya tun daga firamare har zuwa ‘Masters’ ɗina da na yi a kan Public Relation da kuma wadda nake yi a kan Communication Research.

Amma a yanzu gwagwarmayar da na sa gaba ita ce ta kulawa da iyali na da kuma bai wa aiki na muhimmanci, domin ni a yanzu ayyuka sun yi min yawa, hannu na yana can yana can. Saboda haka a gwagwarmayar rayuwa ba na iya cewa komai, iyaye na su ne suka yi min komai na rayuwa.

To yanzu mene ne burin ki a nan gaba?
Buri na shi ne na ga na rabu da iyayena lafiya kamar yadda na rabu da mahaifina lafiya (Allah ya sada shi da rahama) kuma ina son in taimaka wa mata da yara musamman matan da aka ci zarafin su aka yi masu fyaɗe, sannan ina son in taimaka wa mata yan’uwana, domin rayuwar su tana buƙatar kulawa saboda mata suna da rauni don haka ina da burin na ga rayuwar su ta yi kyau ta inganta.

Ki na da burin kafa wata gidauniya a nan gaba?
Ina da tunanin kafa gidauniya sai dai matsala ta guda ɗaya ce, bana son a yayata manufofina, na fi son na yi ta a cikin sirri domin bana son na yi riya, na fi son komai a cikin sirri kamar yadda mahaifina ya yi wa jama’a a Kazaure. Zan bi mata har gidajen su na koya masu sana’a, na taimaka masu da wajen koyar da su sana’a domin su dogara da kansu, yayin da su kuma ƙananan yara zan samar masu da aikin yi inda su ma za su dogara da kansu. Wannan ya na da ga cikin mafarki na, amma ban fara ba, sai nan gaba.

Kamar ƙasashe nawa ki ka taɓa ziyarta?
Na je ƙasashe kamar su Dubai, Saudi Arabia, Sudan, Chadi, Nijar da kuma Turkiyya. Amma a duk ƙasashen da na je ba kamar ƙasar Saudiyya, musamman Madina, a nan ne hankali na ya fi kwanciya. Na fi samun natsuwa, saboda a nan ne fiyayyan halitta yake da zama. Zamana a Madina ya fi min ko’ina a duniya, domin na fi jin daɗin can fiye da ko’ina ƙwarai da gaske.
Me ki ka fi tsana a rayuwar ki?
Ba na son ƙazafi, ba na son a ce na yi abu alhalin ban yi ba.

Me ki ka fi so a rayuwar ki?
Na fi son na ganni kusa da mahaifina lokacin ya na raye, yanzu kuwa na fi son na ganni kusa da mahaifiya ta. Na ganta ta na cikin farin ciki, ba na son na ganta a cikin damuwa ko kaɗan.
Batun abinci fa me ki ka fi so?
Ni mace ce da na ke son girki kala-kala, ina son shinkafa da miyar kifi ko sakwara.

A ɓangaren kwalliya me ki ka fi sha’awar sanyawa?
Na fi son shigar atamfa duk da haka na fi son zani da riga da ɗankwali, kuma na fi son nasa manyan kaya, bana son saka matsattsun kaya, domin idan na sa kaya manya hankalina ya fi kwanciya. Kuma batun lulluɓi na fi son nasa shirgegen hijabi wanda zai rufe min jikina gaba ɗaya.

Ina batun aure?
Ina da aure, muna tare da mijina da yara biyar.

Wane kira za ki yi ga mata ‘yan’uwanki mata?
Ya kamata mata su miƙe sosai wajen neman ilimin addini, kuma mu riƙa taimaka wa mazajen mu domin matan su dogara da kansu domin idan suka dogara da kansu za su samu damar agaza wa mazajen su.

Mata an san ku da kishi, yaya batun hakan take a gare ki?
Shi kishi halitta ne, amma abinda yake faruwa laifin maza ne, saboda sau da yawa mazan ba sa yi wa matansu adalci. Su na nuna bambanci shi ya sa sau da yawa waɗansu abubuwan suke faruwa. Saboda haka don Allah su guji wulaƙanta iyalansu, hakan shi ne yake sawa a samu matsala. Kamata ya yi ko wacce mata mijinta ya bata kulawa kamar yadda yake baiwa ko wacce mace daga cikin matansa. A gaskiya ni ma bana son kishiya duk da cewar kowa da halin sa zai zauna.

Mun gode.
Ni ma na gode sosai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *