Daga IBRAHIM SHEME
Malam Ibrahim Buhari Maidangwale Abdulƙadiri Tubali, wanda aka fi sani da Ibrahim Narambaɗa, fitaccen makaɗin Hausa ne wanda ya rayu a tsakanin wajajen 1890 da Disamba, 1963. Ya yi waƙoƙi masu tarin yawa inda ya wasa sarakuna a ƙasashen Hausa da dama, irin su Zamfara da Maraɗi da Zazzau. Duk da yake a fagen waƙar sarauta ya fi yin fice, ya yi waƙoƙin noma da na ma’aikata (alƙalai) da na ‘yan siyasa irin su Sardauna Ahmadu Bello da na sha’awa (misali waƙar ‘Dokin Iska Ɗanhilinge’). An yi ittifaƙi da cewa ya na da zurfin basira, ta yadda har ana muhawara kan wanda ya fi wani tsakanin sa da Mamman Shata.
Ya na daga cikin mawaƙan Hausa ƙalilan da aka rubuta tarihin rayuwar su ko ake nazarin waƙoƙin su a manyan makarantu saboda gudunmawar da su ka bayar ga ɗorewar al’adun Malam Bahaushe. Saboda farin jinin sa, da wuya rana ta fito ta faɗi ba a sanya waƙar sa a wani gidan rediyo ba. Akwai kuma masu sauraren sa a rediyon motar su ko a komfuta ko a wayar su.
To sai dai kuma Narambaɗa ya kasance makaɗi ɗaya tilo na zamanin sa wanda ba a taɓa ganin hoton sa ba. Hakan ya ɗaure wa mutane da dama kai. An daɗe ana zancen inda za a samu hoton wannan fasihi wanda wasu ke ganin babu ma kamar sa a duk cikin makaɗan Hausa. Ba ma hoto kaɗai ba, babu wasu muhimman bayanan a kan mashahurin mawaƙin duk da yake an yi wasu rubuce-rubucen a kan sa. A gaskiya, abin baƙin ciki ne a samu irin wannan wagegen giɓin game da mutum irin wannan wanda ba a zamanin Annabawa aka yi shi ba.
Da alama, masana kan rayuwa da waƙoƙin Narambaɗa irin su Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza na Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo da Ɗanmadamin Birnin Magaji, Alhaji Ibrahim Muhammad Birnin Magaji, wanda tsohon kwamishina ne kuma ɗan siyasa a Jihar Zamfara, da kuma manyan masoyan Narambaɗa irin su Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, duk sun ƙure tunanin su kan yadda za a samu wannan hoto, amma haƙar su ba ta cimma ruwa ba. Wanda ya fi kowa yin zurfi a wannan haƙa shi ne Farfesa Bunza, wanda har Ingila ya je a cikin 2007 ya yi wata ɗaya kan binciken tarihin Narambaɗa; to ko shi ɗin ma bai cimma ruwa ba. Don haka da ya tashi wallafa tarihin sa, hoton babban ɗan mawaƙin wanda ake kira Kurma ya buga a bangon littafin saboda an ce sun yi kama sosai da Narambaɗa kamar an tsaga rama. Shi ma Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau, Kurma ɗin ne aka zana surar sa aka saka cikin tarihin Narambaɗa da ya buga a littafin sa na tarihin mawaƙan Hausa.
Na daɗe ina tunani kan wannan badaƙalar. Shin a ina za a samu hoton Narambaɗa? An je duk inda za a je ba a samu ba kuwa? A gani na, wannan tambayar ta ƙarshe ita ce ya kamata a nema wa amsa. Amsar ita ce: a’a, ba a gama yawon neman hoton ba. Ilimi teku ne, saboda haka gama ninƙaya a cikin sa abu ne mawuyaci ko ga farfessoshi da ‘yan jarida.
Da farko ma dai, me ya sa babu hoton Narambaɗa? Idan mun duba, wannan mawaƙi dai ya rayu ne a zamanin da akwai na’urorin ɗaukar hoto. Duk da yake ba kowa ne ya mallaki kyamara a wancan lokacin ba, amma akwai kyamarori a ofisoshin hukuma da kuma kafafen yaɗa labarai. Shi ya sanya mu ke ganin hotunan mutanen da Narambaɗa ya waƙe, irin su babban ubangidan mawaƙin, wato Sarkin Gobir na Isa, Alhaji Amadu Bawa, wanda Narambaɗa ya ba shekara takwas a haihuwa, da Magajin Shinkafi Ibrahimu Naguraguri, da Alƙali Abu, da sauran su. Mun ga hotunan su a littafin Farfesa Bunza. Akwai kuma hotunan wasu ‘yan Nijeriyar waɗanda su ka gabaci Narambaɗa.
A makaɗa kuwa, akwai hotunan waɗanda ma su ka girme shi irin su Salihu Jankiɗi (1852-1973) da tsararrakin sa irin su Idi Ɗangiwa Zuru (1893-), Abdu Kurna (1899-1962) da waɗanda ya yi ƙanne da su, wato irin su Mamman Sarkin Tafshin Katsina (1911-1990), da waɗanda su ka biyo bayan sa amma sun shafo zamanin sa irin su Aliyu Ɗandawo (1925-1966) da Mamman Shata (1925-1999). Wasu ma har akwai su a bidiyo. Tunda kuwa haka ne, yaya za a ce mutumin da ya rasu a cikin 1963, kamar yadda Farfesa Bunza ya ce (amma Farfesa Gusau ya ce a 1960 ne), babu hoton sa na kati ko na bidiyo, kamar wani aljani?
Ya aka yi aka samu hotunan waɗancan mawaƙan amma shi babu nasa? Narambaɗa ya yi shuhurar da ta isa a ce an ɗauke shi hoto. Ban da kyamarar gwamnati, akwai jaridu da ake bugawa a zamanin sa, irin su Gaskiya Ta Fi Kwabo wadda ake bugawa tun daga 1939 da Nigerian Citizen wadda aka riƙa bugawa daga 1948 har zuwa 1965, da ma wasu jaridun na Larduna.
Bayan haka, Narambaɗa ya halarci wasu daga cikin manyan tarurrukan da aka yi a ƙasar Hausa inda ake ɗaukar hoto. Misali, ya halarci bikin naɗin babban ubangidan sa Sarkin Gobir Amadu Bawa a cikin 1935, sannan ya je Zariya ya yi wa Sarki Ja’afaru (1937-1959) waƙa bisa umarnin Sarkin Gobir, kuma ya yi wa Iyan Zazzau Muhammadu Aminu waƙoƙi aƙalla guda biyu a lokacin. Bayan haka, akwai alamar ya sake komawa Zariya inda ya halarci naɗin Muhammadu Aminu a matsayin Sarkin Zazzau a cikin 1959, domin kuwa ya yi wa sabon Sarkin waƙar hawan karaga da ma wasu waƙoƙin.
Bugu da ƙari, da wuya a ce Naramaɗa bai taɓa halartar ko da ɗaya daga cikin ɗimbin tarurrukan gasar sukuwa da aka riƙa yi ba inda dokin Sarkin Gobir, wato Ɗanhilinge, ya riƙa yin zarra, ganin irin shaƙuwar da ya yi da dokin.
Wani abin tambaya kuma shi ne a ina aka ɗauki waƙoƙin Narambaɗa da mu ke ji a yau? A littafin tarihin da ya rubuta, Farfesa Bunza bai faɗa mana yadda aka yi aka ɗauki waɗannan waƙoƙin ba. Ya dai faɗa mana cewa an taskace su a gidajen rediyo a Kaduna da Sakkwato da BBC London. To, daga nan ne su ka yaɗu zuwa wasu wuraren, kuma a yau ba a iyakance inda su ka shiga saboda yaɗuwar kayan adana sauti na zamani. Abin da mu ka sani dai shi ne an samu ɗaukar waƙoƙin Hausa ne ta hanyoyi uku: ko dai ta hanyar ofishin yaɗa labarai na gwamnati (irin aikin da su Malam Iro Gawo su ka yi wa Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta Arewa) ko a gidan rediyo, musamman NBC, ko ta hanyar kamfanonin ɗaukar waƙoƙi irin su EMI da Tabansi.
Shin a cikin su wanene ya ɗauki waƙoƙin Narambaɗa, kuma a ina? A Kaduna ko Isa ko Tubali aka ɗauke su? Idan kamfani ne, to su kan ɗauki hoton mawaƙin da su ka ɗau waƙoƙin sa. Ga ire-iren su nan mun gani a fayafayen garmaho. Shin ba su ɗauki hoton Narambaɗa ba ne a irin wannan lokacin?
Idan mun bi zaren tarihin rayuwar Narambaɗa da yadda aka samu ɗaukar waƙoƙin sa a faifai, kamar yadda na zayyana a sama, za mu iya bincikar inda hoton sa ya maƙale. Shin an bincike jaridun da ake bugawa a zamanin Narambaɗa gaba ɗaya ba a ga hoton sa ba? Shin an duba dukkan fayafayen bidiyo da tarin hotunan naɗin sarauta da aka yi a wasu birane da ake jin Narambaɗa ya halarta? An duba hotunan tarurrukan gasar sukuwar dawaki da aka yi a zamanin Narambaɗa kuwa ba a ga hoton sa ba? An duba kowace matattarar aje kayan tarihi da ke ƙasar nan, irin su National Archives da ke Kaduna da na gidajen sarautar da makaɗin ya yi hulɗa da su, ba a ga hoton sa ba?
Babu wani Baturen mulki ko matafiyi da ya ɗauki hoton Narambaɗa? A soshiyal midiya, na ga inda wani ya ce ya taɓa jin cewa akwai hoton Narambaɗa a Jamus, wai wani Bature ne ya ɗauke shi hoton. To amma mai bada labarin bai faɗi sunan Baturen ba ko hukumar da Baturen ya yi wa aiki ko makarantar da aka adana hoton. Idan kuma a cikin laburaren magada ne, to ta ina za a fara neman hoton?
To kuma kada mu yaudari kan mu, mu ce ala tilas akwai hoton Narambaɗa a duniyar nan. Ta yiwu ma ba a taɓa ɗaukar shi hoto ba! Mu tuna, akwai mutane har yau ɗin nan waɗanda ba su yarda a ɗauke su hoto. Wasu ma na danganta abin da addini. Ta yiwu Narambaɗa ya aza aƙidar ƙin yarda da ɗaukar hoto, don haka bai tsaya an ɗauke shi ba. To kuma ta yiwu an ɗauke shi ɗin ba tare da sanin sa ba, musamman a wajen wani taro.
Batun neman hoton Narambaɗa ya na cike da ji-ta-ji-ta da wawuke-wawuke. Amma wannan bai isa ya karya mana gwiwa ba. Ya kamata masu sha’awar wannan batun su tashi tsaye, su ba ƙwaƙwalwa da ƙafafu aikin yi. A tashi daga zaman hirar maganar, a shiga aiki. Na tabbatar idan har an ɓata hankalin dare, to haƙa za ta cimma ruwa.
Idan kowa ya naɗe hannu, ya ƙi taɓuka komai, to ba mu yi wa ‘yan baya waɗanda za su so a ce mun warware masu wannan ƙulli adalci ba. Zamani na ƙara tsawo, damar da ake da ita ta binciko haƙiƙanin gaskiyar al’amari ta na ƙara suɓucewa; shi ya sa wasu al’amuran na ƙasar Hausa ke cike da almara da kame-kame, domin ba a taskace tarihin su na dahir ba. Tun tuni ya kamata manazarta su taimaka a kan wannan batu na hoton Narambaɗa. Lokaci ya kusa wucewa. Yanzu ya kamata a yi a gama a wuce wajen.