INEC: Mu na ci gaba da aiki da lokutan da mu ka tsara na rajistar masu zaɓe

Daga UMAR M. GOMBE

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce ta na nan kan bakan ta na yin aiki da jadawalin da ta tsara na ci gaba da aikin rajistar masu zaɓe daga ranar 28 ga Yuni a duk faɗin ƙasar nan.

Mista Festus Okoye, wanda shi ne Babban Kwamishinan INEC mai kula da wayar da kan masu zaɓe da yaɗa labarai, shi ya bayyana haka a wata hira da ya yi da Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN) a Abuja ran Lahadi.

Okoye ya ce hukumar na nan kan bakan ta, musamman da yake ta samu gidan yana wanda za a yi amfani da shi a wajen aikin.

Ya ce, “An kusa kammala gina gidan yanar yin rajista ta hanyar intanet kuma za a yi aiki da shi wajen yin rajistar masu zaɓe wanda za a fara a ranar 28 ga Yuni.

“An gwada gidan yanar an yi ‘yan gyare-gyare. Zai kasance ya na da maganaɗisun da ke nuna yankunan da ake yin rajista da kuma rumfunan zaɓe.

“Hukumar na ci gaba da aikin ta kuma ta na aiki a cikin tsarin da ta yi na lokuta.”

Hukumar NAN ta ruwaito cewa INEC ta riga ta tsaida 28 ga Yuni a matsayin ranar da za ta ci gaba da aikin rajistar masu zaɓe wanda ta ɗage a baya, kuma ta shigo da sabuwar hanyar kimiyya.

Kwamishinan ya kuma lissafa wasu muhimman ayyuka waɗanda za a yi a cikin lokutan da aka tsara, kafin a kai ga ci gaba da aikin rajistar.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya riga ya bayyana cewa za a ci gaba da aikin har zuwa kashi na uku na shekarar 2022.

Haka kuma Yakubu ya bayyana cewa hukumar za ta maye gurbin tsofaffin na’urorin ɗaukar bayanai kai-tsaye, wato ‘direct data capture (DDC) machine,’ waɗanda aka shigo da su a cikin 2011, don yin rajistar masu zaɓe, da sabuwar hanyar fasaha mai suna ‘INEC Voter Enrolment Device’ (IVED).

A cewar sa, waɗannan sun haɗa da faɗaɗa hanyoyin da masu zaɓe za su samu rumfunan zaɓe ya zuwa ranar 11 ga Mayu, da gina tare da gwada gidan yanar yin rajista ya zuwa ranar 15 ga Mayu da kuma isowar sababbin na’urorin IVED ya zuwa ranar 31 ga Mayu.

Ya lissafa wasu ayyukan da su ka haɗa da ɗaukar ma’aikatan rajistar aiki tare da horar da su, ya zuwa 14 ga Yuni, da kuma ci gaba da aikin rajistar a ranar 28 ga Yuni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *