INEC ta ƙaddamar da zauren tattara sakamakon zaɓen Shugaban Ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Hukumar Zaɓe na Ƙasa INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya ayyana buɗe zauren karɓar sakamakon zaɓen Shugaban Ƙasa na 2023 a hukumance.

Shugaban na INEC ya ce za a fara tattara sakamakon ne daga gundumomi zuwa ƙananan hukumomi, daga nan sai a kai matakin jiha.

Ya ce bayan nan ne kuma za a kai sakamakon zuwa Abuja, babban birnin tarayya, a zauren tattara sakamakon.

Yakubu ya ce baturen zaɓe idan ya zo sanar da sakamakon zaven jihar da ya zo da ita, zai faɗi ta yadda kowa zai ji, inda zai faɗi yawan mutanen da aka yi wa rajista da waɗanda suka samu damar kaɗa ƙuri’a da kuma ƙuri’un da suka vaci.

Shugaban na INEC ya ce bayan haka baturen tattara sakamakon zaɓen kowace jiha zai faɗi yawan ƙuri’un da kowace jam’iyya ta samu, sannan sai a kira wakilan jam’iyya su zo su sanya hannu idan suka amince da sakamakon.

Shugaban na INEC ya yi kira ga dukkan wakilan jam’iyyu da kuma ‘yan jarida da su tabbatar da cewa sakamakon zaɓen da hukumar ta sanar kaɗai za su yaɗa.

Ya ƙara da cewa babu wani wuri da ake sanar da sakamakon zaɓen illa babban zauren da aka tanada.

Yanzu dai an tafi hutun har zuwa ƙarfe shida na yamma lokacin da za a dawo domin fara sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar gadan-gadan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *