INEC ta ɗage tattara sakamakon zaɓen Shugaban Nijeriya zuwa Litinin

Daga SANI AHMAD GIWA

Shugaban Hukumar Zaven Nijeriya Farfesa Mahmood Yakubu ya ɗage zaman tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasar zuwa ranar Litinin.

Farfesa Mahmood ya bayyana hakan ne bayan gabatar da sakamakon jihar Ekiti a zauren tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da ke Abuja babban birnin ƙasar.

Shugaban na INEC ya ce kasancewar jihar Ekitin ce kaɗai ta kai sakamakonta zuwa zauren tattara sakamakon zuwa yanzu, hukumar ta ɗage karvar sakamakon zuwa ranar Litinin da misalin ƙarfe 11:00 na safe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *