INEC ta ɗage zaɓen gwamna zuwa Lahadi a rumfunan zaɓe 10 a Legas

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta ɗage zaɓen gwamna da na majalisar jiha a wasu rumfunan zaɓe guda 10 a yankin Lekki, Jihar Legas.

Kwamishinan INEC na jihar, Segun Agbaje, shi ne ya sanar da haka ga manema labarai.

A cewarsa, wasu masu yi wa ƙasa hidima da INEC ta ɗauka aikin wucin-gadi sun yi zargin an kama su yayin zaɓen Shugaban Ƙasa da ya gabata yayin da suka yi yinƙurin shiga yankin.

Ya ce bayan da ma’aikatansu suka shirya kayan aiki, mazauna yankin sun ji tsoron fitowa gudun kada ɓata-garin yankin su fafare su, su tarwatsa shirin, wanda hakan ya hana zaɓe gudana a yankin.

“Bayan tuntuɓar hedikwatar hukumar da aka yi, ta ba da umarnin a dawo gobe (Lahadi) da safe don gudanar da zaɓen.

“Don haka gobe (Lahadi) da safe za mu haɗu a yankin mu gudanar da zaɓe,” in ji Kwamishinan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *