INEC ta ɗage zaɓen gwamnoni da na majalisun jihohi da mako guda

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta kammala shirinta don ɗage zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi wanda ta shirya gudanarwa ran 11 ga Maris.

Yadda al’amarin yake yanzu, shi ne, INEC ta ɗage zaɓe da mako guda zuwa ranar 18 ga Maris, 2023, kamar yadda wata majiya mai tushe ta shaida wa Jaridar News Point Nigeria.

Manhaja ta gano ɗage zaɓen na da nasaba da gazawar INEC wajen saita na’urar BVAS ɗin da aka yi amfani da su a zaɓen ranar 25 ga Fabrairu don sake yin amfani da su wajen gudanar da zaɓen gwamnoni.

Majiya ta kusa da INEC ta ce shugabannin hukumar sun yi taro inda a nan ne aka cimma matsayar ɗage zaɓen walau zuwa ran 18 ko 25 ga Maris.

Amma a ƙarshe taron ya amince da ɗage zaɓen zuwa 18 ga Maris.

“Kun san cewa sake saita BVAS zai ɗauki kwana uku ko huɗu, tun da baki ɗaya za a kwashe ne zuwa hedikwata a Abuja, za a sake saita na’urorin sannan a tura su jihohi, sannan zuwa rumfunan zaɓe,” in ji ɗaya daga cikin jami’an hukumar.