INEC ta amince da tsawaita shirin rijistar masu zaɓe da kwana 60

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta amince da tsawaita wa’adin gudanar da shirin yi wa masu zaɓe rijista da kwana 60.

Kafin wannan lokaci, ƙarshen watan Yunin 2022 INEC ta tsayar a matsayin lokacin da za ta kammala shirin yi wa masu zaɓe rijista.

Jaridar Guardian ta rawaito cewa, Shugabar Kwamitin Majalisar Wakilai Kan Saha’anin Zaɓe, Aishatu Jibril Dukku ce ta bayyana tsawaita wa’adin ga takwarorinta a ranar Laraba.

Ta ce, “Jiya (Talata) Kwamitin ya gana da INEC inda aka amince da batun tsawaita shirin yin rijistar…..”

A ranar Litinin da ta gabata wata Babbar Kotun Abuja ta taka wa INEC burki game da ƙudurinta na rufe shirin yin rijistar ya zuwa 30 ga Yuni, 2022.

Da wannan, dama ta sake samu ga ‘yan Nijeriyar da ba su riga sun mallakin katin zaɓensu ba su yi hakan.