INEC ta bayyana Soludo a matsayin wanda ya lashe zaɓen Anambara

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana Farfesa Chukwuma Soludo na jami’iyyar APGA a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Anambara da aka gudanar ran 6 ga Nuwamba.

Bayan ƙidayar ƙuri’u, INEC ta ce ƙuri’u 112,229 Soludo ya samu wanda hakan ya ba shi nasara a kan ɗan takar PDP, Mr Valentine Ozigbo wanda ya samu ƙuri’u 53, 807, wato shi ne dan takara na biyu mai mafi yawan ƙuri’u.

Sai kuma ɗan takarar APC,
Sanata Andy Uba da ya zo na uku da ƙuri’u 43,285.

Malamar zaɓen, wato Farfesa Florence Obi, ita ce ta bayyana wannan sakamako da safiyar Laraba a babban ofishin INEC da ke Awka.

Tun farko Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa sai da INEC ta dakatar da tattara sakamakon zaɓen ran Lahadi da daddare tare da ayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammalu ba biyo bayan rashin zaɓe a yankin ƙaramar hukumar Ihiala.

Amma daga bisani hukumar ta tsayar da ranar Talata, 9 ga Nuwamba a matsayin ranar da za a gudanar da zaɓe a yankin Ihiala wanda bai yiwu ba a baya.

Sa’ilin da take bayyana sakamakon ƙarshe na zaɓen, Obi ta ce bayan da aka haɗa sakamakon zaɓen Ihiala, nan ne Soludo ya ci gaba da samun yawan ƙuri’u sama da takwarorinsa. Tare da cewa, Soludo ya samu nasarar lashe ƙananan hukumomi 19 cikin 21 da jihar Anambara ke da su.

Yankunan da Soludo ya lashe zaɓensu kamar yadda Obi ta lissafo, sun haɗa da; Dunukofia, Awka ta Kudu, Oyi, Anaocha, Ayamelum, Anambra ta Gabad, Idemili ta Kudu, Onitsha ta Kudu da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *