INEC ta buƙaci Majalisar Tarayya ta maida guraben zaɓe zuwa rumfunan zaɓe

 Daga WAKILINMU


Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi kira ga Majalisar Tarayya da ta amince mata ta mayar da ƙananan guraben kaɗa ƙuri’a da ke faɗin ƙasar nan zuwa cikakkun rumfunan zaɓe.
 
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya yi wannan roƙon a lokacin da ya gabatar da bayani kan yadda za a sama wa masu zaɓe rumfunan kaɗa zaɓe (wato Pulling Units, PUs) a Nijeriya, a gaban Cikakken Kwamitin Majalisar Tarayya kan Hukumar Zaɓe da Al’amuran Zaɓe, a ranar Talata a Abuja.
 
Ya ce wasu daga cikin guraben kaɗa ƙuri’ar idan aka maida su rumfunan zaɓe, za a kuma ɗauke su zuwa wuraren da aka fi buƙatar su.

Haka kuma Yakubu ya yi kira ga ‘yan majalisar da masu ruwa da tsaki cikin lamarin da su taimaka su cire batutuwan siyasa daga cikin manufar hukumar, ya na mai cewa al’amarin ya shafi dukkan sassan ƙasar nan.
 
Ya ce samun wurin jefa ƙuri’a ga mutanen ƙasar nan ya shiga mugun yanayi a yanzu domin kuwa rumfunan zaɓe da ake da su a yau guda 119,973 tsohuwar Hukumar Zaɓe ta Nijeriya (NECON) ita ce ta samar da su shekaru 25 da su ka gabata.

Ya yi nuni da cewa a wancan lokaci an ƙiyasta cewa rumfunan zaɓen da ake da su yanzu za su yi wa masu zaɓe miliyan 50 da su ka yi rajista aiki ne, to amma sun ƙaru zuwa sama da mutum miliyan 84 a cikin 2019 kuma ana sa ran za su ƙaru kafin manyan zaɓuɓɓukan da ke tafe.

Yakubu  ya ce ban da ƙarancin da rumfunan zaɓen su ka yi a yanzu, akwai kuma rashin dacewar su ga masu zaɓe, musamman ganin ana cikin yanayin annobar korona yanzu.

Ya ƙara da cewa ita ma Hukumar Zaɓe ta na shan wahala wajen gudanar da zaɓe cikin adalci da bin doka da oda a waɗannan rumfunan.
 
Shugaban hukumar ya ce INEC ta sha yin ƙoƙarin magance matsalar a baya amma ‘yan Nijeriya ba su fahimtar manufar ta saboda rashin wayar masu da kai kuma da yake ana ɗaukar matakan ne a daidai lokacin da zaɓe ya ƙarato.

A cewar Yakubu, wasu daga cikin matakan da hukumar ta ɗauka don magance matsalar sun haɗa da ƙirƙiro ƙananan wuraren zaɓe a cikin 2007, da guraben kaɗa ƙuri’a a cikin 2011 da kuma unguwannin guraben zaɓe a Yankin Birnin Tarayya a cikin 2016.

Ya ce hukumar ta yi amanna da cewar idan aka maida ƙananan guraben zaɓe da ake ta amfani da su tun cikin 2011 zuwa rumfunan zaɓe tare da sauya wa wasun su matsuguni zuwa inda ya dace, to yawancin ƙalubalen da masu zaɓe da ita kan ta hukumar su ke fuskanta za su kau.

Yakubu ya ce ban da fara aiki da wuri kan batun da hukumar ta yi a yanzu, haka kuma hukumar ta yanke shawarar ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da waɗanda ke da ruwa da tsaki cikin lamarin don magance wannan matsala da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.
 
Ya bayyana cewa ya zuwa yanzu har hukumar ta samu sama da buƙatu 9,000 daga unguwanni da ɗaiɗaikun mutane a faɗin ƙasar nan na a ƙirƙiro masu rumfunan zaɓe.

“Mun samu kiraye-kiraye guda 5,747 a cikin Oktoba 2020 na mu kafa sababbin rumfunan zaɓe. Ba hukumar mu ba ce ta faɗa wa mutane cewa su rubuto buƙatar su ta a ƙirƙiro masu rumfunan zaɓe ko wani abu makamancin hakan.
 
“Ya zuwa makon jiya, 23 ga Fabrairu, yawan buƙatun ya ƙaru zuwa 9,092, wanda ya nuna ƙaruwar 4,300 a cikin watanni huɗu kuma har yanzu yawan ya na ci gaba da ƙaruwa,” inji shi.

Ya bada tabbacin cewa idan aka maida ƙananan guraben zaɓen zuwa rumfunan zaɓe, hukumar za ta yi la’akari da yawan masu zaɓe da su ka yi rajista a kowace rumfar zaɓe da kuma tazarar da ke tsakani, don tabbatar da cewa an yi adalci kuma an magance matsalar sosai.

A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Dattawa,
Sanata Ahmad Lawan, ya yi alƙawarin cewa Majalisar Tarayya za ta mara wa INEC baya wajen samar da yanayin zaɓe mafi nagarta ga ‘yan Nijeriya ta hanyar ƙirƙiro ƙarin rumfunan zaɓe.
 
Lawan ya ce, “Ina so in tabbatar wa da Shugaban Hukumar Zaɓe da ma ‘yan Nijeriya cewa Majalisar Tarayya za ta ba INEC cikakken goyon baya, ba tare da inda-inda ba, don tabbatar da mun samar da yanayin zaɓe mafi inganci ga mutanen ƙasar mu.

“Za mu yi dukkan abin da ya dace, domin manufar mulkin dimokiraɗiyya ita ce a ba kowa dama kuma zaɓe shi ne kusan abin da ya fi komai muhimmanci.”
 
Yakubu ya samu rakiyar kwamishinonin ƙasa da wasu daga cikin jami’an gudanarwa na hukumar zuwa majalisar.