INEC ta dakatar da ci gaba da tattara sakamakon zaɓe a jihohin Abia da Enugu

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta ba da sanarwar dakatar da ci gaba da tattara sakamakon zaɓe a jihohin Enugu da Abia.

Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Kwamishinan INEC, Barista Festus Okoye, ya fitar a ranar Litinin.

Wannan na zuwa ne bayan da ‘yan baranda suka farmaki ofishin hukumar a yankin Ƙaramar Hukumar Obingwa inda aka yi garkuwa da wasu jami’an zaɓen.

A cewar sanarwar, “Hukunar ta yi zama yau Litinin, 20 ga Maris, 2023 inda ta yi nazarin zaɓen gwamna da na majalisar jihar da ya gudana a jihar ranar Asabar, 18 ga Maris, 2023.

“Yayin zaman hukumar ta yanke shawarar dakatar da ci gaba da tattara sakamakon zaɓen a wasu sassan jihohin Abia da Enugu.

“Idan za a iya tunawa, ‘yan baranda sun kai farmaki a ofishinmu na Ƙaramar Hukumar Obingwa jiya Lahadi, 19 ga Maris, 2023 kuma an kama wasu jami’anmu dangane da tattara sakamakon zaɓe a yankin.”