INEC ta dakatar da Kwamishinan Zaɓe na Adamawa, Yunusa Ari

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta dakatar da Kwamishinan Zaɓe na Jihar Adamawa, Hudu Yunusa Ari.

Dakatarwar na da saba da bayyana ‘yar takarar Gwamna ta Jam’iyyar APC a jihar, Aisha Dahiru Binani, da Kwamishinan ya yi a matsayin wadda ta lashe zaɓen gwamnan jihar yayin zaɓen cike giɓin da ya gudana a ranar Asabar a jihar.

Cikin wasiƙar da hedikwatar INEC ta fitar a ranar Litinin, hukumar ta umarci Ari da ya yi nesa da ofishin hukumar da ke Yola, babban birnin jihar.

Wasiƙar mai ɗauke da kwanan wata 17 ga Afrilu, 2023, da kuma sa hannu Sakatariyar INEC, Rose Oriaran-Anthony, ta umarci Sakataren Gudanarwa na humar a Yola ya ci gaba da riƙe hukumar.

Babban ofishin na INEC ya nuna rashin jin daɗinsa kan riga-malam-masallacin da Ari ya yi wajen bayyana wanda ya lashe zaɓe tun kafin kammala tattara sakamakon zaɓe.

Lamarin da ya sa INEC ta soke bayyanarwar tare da ɗage ci gaba da tattara sakamakon zaɓen na gwamnan Adamawa.