INEC ta fara ɗora sakamakon zaɓe a intanet ta BVAS

Daga SANI AHMAD GIWA

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta ɗora wasu daga cikin sakamakon zaɓen ranar Asabar ta hanyar BVAS.

Rashin amfani da BVAS a zaɓen ranar 25 ga Fabrairu ya haifar da dambarwar amincewa ga hukumar zaɓen, wanda ‘yan Nijeriya da jami’an zave suka yi kakkausar suka.

Kodayake hukumar ta yi amfani da matsalar fasaha a matsayin dalilin rashin amfani da BVAS wajen watsa sakamako, da yawa masu suka sun ƙi amincewa da uzurin.

Sai dai hukumar ta yi alƙawarin inganta tare da yin amfani da na’urar a zaɓen da ke gudana yau.

Manhaja ta lura cewa an saka sakamakon mazaɓar 001 mai lamba 039 a ƙaramar hukumar Yenagoa a Bayelsa ta BVAS da misalin ƙarfe 1:58 na rana.

A zaɓen majalisar wakilai, Jam’iyyar APC ta samu ƙuri’u shida yayin da Jam’iyyar PDP ta samu ƙuri’u 13.

Bayelsa na ɗaya daga cikin jihohin da babu gwamna sai zaɓen ‘yan majalisar jiha.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *