INEC ta fara miƙa shaidar lashe zaɓe ga zaɓaɓɓun gwamnoni

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta fara miƙa shaidar lashe zaɓe ga ‘yan takarar da suka ci zaɓen gwamna a jihohinsu.

Zaɓaɓɓun gwamnoni a jihohi 26 ne INEC ta tabbatar da nasarar da suka samu a zaɓen da ya gudana ranar 18 ga Maris, 2023.

Kazalika, INEC za ta miƙa shaidar lashe zaɓe ga ‘yan majalisar jihohi da suka samu nasarar yayin zaɓen a jihohi 36.

Sanarwar da Kwamishinan INEC, Festus Okoye, ya fitar ranar Asabar, ta ce Sashe na 72(1) na Dokar Zaɓe na 2022 ya nuna haƙƙi ne a kan INEC ta miƙa shaidar lashe zaɓe ga dukkan ‘yan takarar da suka yi nasara bayan zaɓe da kwana 14.

Kazalika, ta ce INEC ta tsayar da ranar Laraba (yau ke nan) da kuma Juma’a mai zuwa a matsayin ranakun da za ta miƙa shaidar lashe zaɓen ga waɗanda lamarin ya shafa.

Ta ƙara da cewa, miƙ shaidar zai gudana ne a babban ofishin INEC a jihohi.