INEC ta fitar da jadawalin ranakun rajistar masu zaɓe

Daga WAKILINMU

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana ranaku da abubuwan da za a yi dangane da rajistar masu jefa ƙuri’a da ake gudanarwa a yanzu.

Idan kun tuna, an fara aikin ne daga ranar 28 ga Yuni, 2021 kuma za a ci gaba da yin sa har zuwa ranar 11 ga Yuli, 2022.

A sanarwar da sashen yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe na hukumar ya fitar, an nuna cewa za a yi aikin a watanni uku na farko da watanni uku na biyu na wannan shekarar da mu ke ciki.

A baɗi kuma za a yi aikin a watanni uku na biyu da watanni uku na huɗu na shekarar.

Jadawalin ya nuna cewa a bana, daga 28 ga Yuni zuwa 21 ga Satumba za a gudanar da rajistar masu zaɓe.

Daga ranar 28 zuwa 30 ga Satumba kuma za a kafe sunayen waɗanda su ka yi rajista domin kowa ya duba domin tabbatar da bayanan sa da aka wallafa daidai ne ko kuma akwai gyara.

Aiki na gaba shi ne ci gaba da aikin rajistar masu zaɓe wanda za a fara a ranar 4 ga Oktoba, kuma a ci gaba da yin sa har zuwa ranar 20 ga Disamba, 2021.

A shekarar 2022 kuma, INEC za ta ci gaba da rajistar masu zaɓe a ranar 3 ga Janairu, sannan za ci gaba da yi har zuwa ranar 22 ga Maris.

Daga nan za a dakata domin kafe sunayen waɗanda su ka yi rajistar saboda su duba su tabbatar da bayanan su da aka wallafa daidai ne ko kuma akwai gyara.

Za a yi hakan ne a tsakanin ranar 26 ga Maris zuwa ranar 1 ga Afrilu, 2022.

A tsakanin ranar 11 ga Afrilu zuwa ranar 30 ga Yuni kuma za a ci gaba da gudanar da aikin rajistar masu zaɓe.

Sa’annan, kamar dai yadda aka yi a baya, za a kafe sunayen waɗanda su ka yi rajistar saboda tabbatar da ingancin su da yin gyare-gyare a inda ya dace.

Bugu da ƙari, INEC ta bayyana irin mutanen da za su iya zuwa ofishin yin rajistar.

A cewar ta, kowane ɗan Nijeriya da ya kai ɗan shekara 18 ya cancanci yin rajistar zaɓen idan har bai taɓa yin rajista a baya ba.

Haka kuma shi ma duk wanda ya taɓa rajista amma ya samu wata matsala da rajistar sa a zaɓuɓɓukan baya, wadda ya ke so a gyara masa a yanzu, shi ma zai iya zuwa.

Hukumar ta kuma ce idan mutum mai rajista ya na so a sauya masa wurin da zai kaɗa ƙuri’a zuwa wani wajen, shi ma zai iya zuwa a gyara masa.

Haka kuma duk wanda ya yi rajista amma katin sa ya ɓace ko ya lalace, shi ma zai iya zuwa a ba shi sabon katin rajistar zaɓe.

Shi ma wanda ke so a gyara masa wani bayani da aka yi masa rajista da shi a baya, kamar suna ko ranar haihuwa, to shi ma zai iya zuwa ofishin rajistar domin a gyara masa, inji hukumar.

A ƙarshe, hukumar ta bada sanarwar cewa za a ɗage aikin rajistar a Jihar Anambra a cikin Agusta 2021 saboda zaɓen gwamnan jihar da za a yi a ranar 6 ga Nuwamba, 2021.