INEC ta gano rijistar katin zaɓe mara kyau sama da miliyan 1.3

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce, ta gano rijistar katin zaɓe mara kyau guda 1,390,519 da aka yi a shirin rijisar katin zaɓen (CVR) da ke gudana a halin yanzu.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka ga manema labarai ranar Laraba a Abuja, yana mai cewa wannan adadi daidai yake da kashi 45 na katin zaɓe 2,523,458 da aka kammala yin rijistarsu.

Yakubu ya ƙara da cewa, wannan adadi ɓangare ne na rijistar da aka kammala daga Yunin 2021 zuwa 14 ga Janairun 2022.

KARANTA: ‘Yan fashin daji sun yi awon gaba da ɗaliban Zamfara

Ya ci gaba da cewa kawo yanzu, Nijeriya ta shiga zango na huɗu kenan a ci gaba da shirin yi wa masu kaɗa ƙuri’a rijista wanda ya kankama a ranar 28 ga Yunin 2021 bayan da aka ɗan dakatar da shirin albarkacin babban zaɓen 2019.

Shugaban INEC ya ce wannan al’amari abin damuwa ne, tare da bada misalin hakan kan faru ne sakamakon yin rijista fiye da sau guda, gazawar na’urar aiki da kuma rashin ɗaukar cikakkun bayanan mutum.

Haka nan, ya ce wannan matsalar ta shafi dukkan jihohin ƙasa, kana ya jaddada cewa ba za a sanya rijista mara kyau a cikin lissafin masu kyau ba.

Daga nan, Yakubu ya bayyana farin cikinsa kan adadin sabbin rijistar da aka yi wa jama’a, sannan ya ƙarasa da cewa Hukumar Zaɓe za ta yi aikinta yadda ya kamata wajen tabbatar da ‘yan Nijeriyar da suka cancanta kaɗai za a yi wa rijista.