INEC ta koka: ’Yan siyasa na sayen katin zaɓe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce, wasu ’yan siyasa su na sayen Katin Zaɓe na Dindindin (PVC) daga hannun masu kaɗa ƙuri’a.

Mohammed Haruna, muƙaddashin kwamishinan INEC na ƙasa mai kula da babban birnin tarayya Abuja, Nasarawa, Kaduna da Filato, ya bayyana haka a ranar Litinin yayin ƙaddamar da shirin ‘VoteMatters’ na NESSACTION a Abuja.

Kamar yadda aka ruwaito, Haruna ya ce, hukumar zaɓe na kai farmaki kan ’yan kasuwar bayan fage masu sayar da Katin Zaɓe.

“Muna sane da cewa wasu ’yan siyasa sun duƙufa sayen katunan zaɓe. Ba daidaj bane mutane su riƙa karɓar katin zaɓe sannan su sayar da shi ko barin wani ya kasance ana amfana da shi ba bisa ƙa’ida ba wanda laifi ne a cikin Dokar Zaɓenmu.

“Wasu daga cikin mutane na sane da cewa kwanan nan, wasu mutane biyu da aka samu da laifin mallakar katunan zaɓe a Kano da Sokoto, INEC ta yanke musu hukunci. Don haka ina kira ga jama’a da su tattara katunansu, su adana su ta yadda a ranar zaɓe za su fita su kaɗa ƙuri’a, domin kuwa idan ba kati, mutum ba zai iya zaɓe ba,” inji shi.

A halin da ake ciki, an fara tattara na’urorin PVC a faɗin ƙasar a ranar Litinin a ofisoshin ƙananan hukumomi da ke faɗin ƙasar.

Hukumar ta ce, ‘yan Nijeriya za su iya fara karɓar katinsu a wuraren rajista 8,809 daga ranar 6 ga Janairu zuwa 15 ga Janairu, 2023.

Bayan 15 ga Janairu, 2023, atisayen zai koma ofisoshin ƙananan hukumomi har zuwa ranar 22 ga Janairu, 2023.

Masu kaɗa ƙuri’a za su iya karɓar PVC ɗin su daga ƙarfe 9 na safe zuwa ƙarfe 3 na rana, ciki har da Asabar da Lahadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *