INEC ta miƙa wa zaɓaɓɓun ‘yan Majalisar Wakilai shaidar lashe zaɓe

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta miƙa shaidar lashe zaɓe ga ‘yan Majalisar Wakilai da suka lashe zaɓe a zaɓen da ya gudana ran 25 ga Fabrairu.

A ranar Laraba INEC ta miƙa wa ‘yan majalisar shaidarsu a Babban Zauren Taro na Ƙasa da Ƙasa da ke Abuja.

Waɗanda suka yi nasarar sun haɗa da sanatoci 98 daga cikin 109 da ake da su, sai kuma ‘yan Majalisar Wakilai 325 daha cikin 360 da ake da su.