INEC ta sanar da Shekarau a wanda ya lashe zaɓen sanatan Kano ta tsakiya

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta sanar da sunan Malam Ibrahim Shekarau a matsayin wanda ya lashe zaɓen Sanatan Kano ta tsakiya a ƙarƙashin Jam’iyyar NNPP.

Baturen zaɓen Farfesa Tijjani Hassan Darma ne ya bayyana Sanata Shekarau a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙuri’a 456,787 akan babban abokin karawarsa na Jamiyyar APC Abdulkarim Abdussalam Zaura wanda ya sami ƙuri’a 168, 677, da Hajiya Laila Buhari ta jam’iyyar PDP da kuri’a 55,237,

Jim kaɗan bayan kammala faɗin sakamakon wakilin jam’iyyar NNPP ya ƙalubalanci hukumar zaɓe akan kin canja sunan Shekarau wanda tuni ya koma jam’iyyar PDP

A baya dai Sanata Malam Shekarau shi ne wanda Jam’iyyar NNPP ta fara tsayarwa a matsayin dan takararta a kujerar sanatan Kano ta Tsakiya. Yayin da Shekarau din ya koma jam’iyyar PDP kuwa sai aka maye gurbinsa da Sanata Rufa’i Sani Hanga.

Sai dai kuma INEC ta ce har zuwa lokacin da aka gudanar da zaɓen sunan Shekarau ne, kuma ba a canja sunansa ba.