INEC ta shigar da ƙarar kwamishinanta na Adamawa, Hudu Ari, a kotu

Daga MAHDI M. MUH’D

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta a Nijeriya (INEC) ta shigar da tuhume-tuhume shida a gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓe, kan dakataccen kwamishinan zaɓe na Jihar Adamawa, Hudu Yunusa-Ari.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar mai ɗauke da sannun shugaban sashen wayar da kan al’umma na hukumar, Festus Okoye, ta ce an shigar da ƙarar ce a babbar kotun jiha da ke Yola, a Jihar Adamawa.

Sanarwar ta kuma tabbatar da samun takardar kammala bincike kan laifukan da suka shafi zaɓe daga hannun ’yan sanda, bayan kammala bincike kan laifukan zaɓe da aka yi a babban zaɓen na 2023, ciki har da wanda ya shafi Ari.

Sanarwar ta ce, “Kamar yadda sashe na 145(1) na dokar zaɓe ta 2022 ya tanadar, laifin da aka aikata a ƙarƙashin dokar za a iya gurfanar da shi a gaban kotun majistare ko kuma babbar kotun jihar da aka aikata laifin, ko kuma babban birnin tarayya, Abuja.

Bayanin ya ƙara da cewa, kotu ta sanya ranar Laraba 12 ga Yulin 2023 don fara shari’ar.

Yunusa-Ari dai ya shiga matsala ne bayan kammala zaven gwamnan Jihar Adamawa a ranar 15 ga Afrilun 2023, lokacin da ya bayyana Aisha Dahiru ‘Binani’ ta jam’iyyar APC a matsayin wadda ta lashe zaɓen da aka gudanar a yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaɓen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *