INEC ta tsayar da lokacin miƙa wa zaɓaɓɓun ‘yan majalisun tarayya shaidar lashe zaɓe

Daga BASHIR ISAH

Ya zuwa ranakun Talata da Laraba masu zuwa ake sa ran Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta miƙa shaidar lashe zaɓe ga ‘yan majalisun tarayya da suka kai bantensu a zaɓen da ya gudana.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka ranar Asabar da safe yayin taronsu da Kwamishinonin Zaɓe (REC) a Abuja.

Yakubu ya ce ‘yan majalisu 423 ne suka ci zaɓe, yayin da za a sake zaɓen ‘yan majalisu a wasu mazaɓu 46.

Ya ce, ‘yan majalisun da suka ci zaɓen sun haɗa da sanatoci 98 cikin 109, da ‘yan Majalisar Wakilai 325 cikin 360.

“Za a miƙa wa Sanatoci shaidar lashe zaɓe ran Talata, 7 ga Maris, 2023 da misalin ƙarfe 11.00am a Babban Zauren Tattara Sakamakon Zaɓe (wato Babban Zauren Taro na Ƙasa da Ƙasa) da ke Abuja.

“Yayin da su kuma ‘Yan Majalisar Wakilai za a miƙa musu tasu shaidar ranar Laraba, 8 ga Maris, 2023 da misalin ƙarfe 11.00am a nan babban zauren,” in ji Yakubu.

Ya ƙara da cewa, “domin kauce wa cunkoson jama’a yayin taron, mutum biyu aka yarda su yi wa ‘yan majalisun rakiya.”