INEC ta ware Naira biliyan uku don yaƙi a kotunan zaɓe

Daga AMINA YUSUF ALI

Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta ware Naira Biliyan Uku, don kare sakamakon zaɓen Shugaban Ƙasa da na ‘yan Majalisar Dokoki Ta Ƙasa na ranar 25 ga Fabrairu, 2023, da na gwamnoni da ‘yan majalisun dokokin jiha na ranar 18 ga Maris, 2023.

Idan za a iya tunawa dai, ‘yan takara da dama da suka faɗi zaɓen Shugaban Ƙasa da ma jiha sun shigar da ƙararraki a kotunan zaɓe, don ƙalubalantar sakamakon waɗancan zaɓuɓɓuka da kuma neman a soke su.  

A yanzu haka dai akwai ƙararraki fiye da guda 100 a ƙasa waɗanda fusastattun ‘yan takarkarun da suka sha kaye da su da jam’iyyunsu suka shigar a faɗin ƙasar nan. 

Ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP ALlhaji Atiku Abubakar; ɗan takarar LP, Peter Obi; ɗan takarar jam’iyyar AC, Solomon Okangbuan; da ɗan takarar jam’iyyar APM, Chichi Ojei, su ma dukkansun shigar da ƙara don a soke zaɓen da ya gabata.  

Hukumar INEC a ranar Maris, 1 ga wata ta sanar da ɗan takarar jam’iyyar APC, Bola Tinubu, a matsayin wanda ya lashe zaɓen na 25 ga Fabrairu. Sai dai ‘yan takara 5 ne suka shigar da ƙara a kan a soke wancan zaɓen.  

Haka jihohi 12 su ma sun shigar da ƙara da nuna rashin gamsuwa da sakamakon zaɓen Majalisar jiha. su ne, jihohin Edo, Filato, Ondo, Kwara, Ogun, Bayelsa, Oyo, Osun, Ekiti, Bauchi, Legas da Neja.

A wasu jihohin ma har zanga-zangar nuna ƙin amincewa da zaven aka yi.