INEC ta yi gargaɗin akwai gidan yanar rajistar zaɓe na ƙarya

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ja hankalin jama’a dangane da wani gidan yana na ƙarya na yin rajistar zaɓe a intanet.

Hukumar ta yi gargaɗin ne a cikin wata sanarwa da Mista Festus Okoye, Babban Kwamishina kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Faɗakar da Masu Zaɓe na INEC ya fitar a Abuja.

Okoye ya ce an ja hankalin INEC ne zuwa ga wani saƙo da ake yaɗawa a soshiyal midiya game da wani gidan yana da aka ce wai na yin rajistar masu zaɓe na INEC ne “wanda ya sha bamban da ainihin gidan yanar rajistar INEC na gaskiyar.”

Ya ce, “Adireshin gidan yanar ƙaryar shi ne https://register.inec-pvc.online/ wanda ake taƙaitawa kamar haka, https://bit.ly/INEC-PvcReg2021.”

Ya ce, “INEC ta na bayyana cewa ko kaɗan babu ruwan ta da wannan gidan yanar da duk wani abu da ake aikatawa a cikin sa.”

Okoye ya ce INEC ba ta ba kowace hukuma ko ƙungiya aikin ɗaukar bayanan duk wani mai niyyar yin zaɓe a madadin ta ba.

Ya ce, “Ana sanar da dukkan jama’a cewa gidan yanar da INEC ke ci gaba da gudanar da rajistar masu zaɓe a yanar gizo dai shi ne https://cvr.inecnigeria.org.”