Daga MAHDI M. MUUHAMMAD
Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC, ta sanar da ranar fara ba da katin zaɓe na dindindin tare da ƙara gargaɗar masu karya dokokin zaɓe gabanin zaɓen 2023.
Hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu zave na hukumar na ƙasa, Festus Okoye Esq, ya fitar da ranar Asabar a Abuja.
Hukumar ta yi zamanta ne a ranar Asabar 26 ga watan Nuwamba, 2022, inda ta tattauna kan batutuwa da dama da suka haɗa da kwanan wata da tsarin karɓar katin zaɓe na dindindin (PVC) da kuma gurfanar da mutanen da aka kama bisa zargin mallakar katin ba bisa ƙa’ida ba.
Hukumar ta ce, bayan kawo ƙarshen wa’adin da aka ƙayyade na nuna rajistar masu kaɗa ƙuri’a kan ƙorafi da rashin amincewa, Hukumar ta ƙuduri aniyar sanya tarin na’urorin PVC ba tare da wata matsala ba. An ɓullo da Tsarin Aiki SOP. Wannan zai kasance daga cikin batutuwan da za a tattauna tare da kammala su a wani taro na da za a gudanar a Legas daga ranar 28 ga Nuwamba zuwa 2 ga Disamba 2022 wanda ya ha&a da dukkan Kwamishinonin Zaɓe (REC).
A ƙarshen ranar, Hukumar za ta fitar da ranakun da kuma cikakken tsarin da za a bi wajen karɓar katin PVC a faɗin ƙasar nan.
Hukumar ta yaba da haƙuri da fahimtar ’yan Nijeriya musamman waɗanda suka yi rajista a matsayin masu kaɗa ƙuri’a ko kuma suka nemi a canja musu katin daga watan Janairu zuwa Yulin 2022. A wajen samar da katunan na karɓa, hukumar ta kuma duƙufa wajen ganin an gudanar da aikin.
Bugu da ƙari, a cikin makonni biyun da suka gabata rundunar ’yan sandan Nijeriya ta kama wasu mutane da aka samu da mallakar katin zaɓe ba bisa ƙa’ida ba a wasu jihohin tarayyar ƙasar. A wata shari’a, ’yan sanda sun kammala bincike tare da miƙa wa hukumar fayil ɗin ƙarar gurfanar da wani masu suna Nasiru Idris a gaban wata kotun majistare da ke Sokoto wanda aka same shi da katin PVC guda 101 wanda ya saɓa wa sashi na 117 da 145 na dokar zaɓe ta 2002. An yanke masa hukuncin ɗaurin shekara guda a gidan yari.
Hukumar na fatan sake jaddada cewa za ta cigaba da bin diddigin duk waɗanda suka karya dokar zaɓe tare da tabbatar da gurfanar da su a gaban koliya.