INEC tana neman jami’in tattara sakamakon zaɓe a Mafara ruwa a jallo

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Hukuma INEC ta jihar Kebbi tana neman jami’in tattara sakamakon zaɓen mazaɓar Marafa bisa ga batan dabo da ya yi ba tare da ya zo yi sanarwar sakamakon ba.

Tuni hukumar ta saka wani jami’i a wannan mazaɓar ta Marafa da ke Birnin Kebbi a gundumar Kebbi ta tsakiya da ya ke akwai sakamakon hannun wakilan kowace jam’iyya da kuma ita Kanta hukumar zaɓen.